Shugaba Tinubu ya ware Naira miliyan 125 domin kula da fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa a shekarar 2025.
Shugaban ƙasar ya ware Naira miliyan 86 domin kula da dabbobi da kuma Naira miliyan 38.5 na kula da ciyayi da fulawar fadar ta Aso Rock a shekarar.
Kazalika an ware Naira miliyan 165 domin sayen tayoyi masu sulke, baya ga Naira biliyan 4.7 na sayen sababbin motoci.
Kayayyakin motsa jikin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci Naira miliyan 101, a yayin da aka ware Naira miliyan 73 domin sayen na’urorin sadarwa.
- Za a rataye shi saboda kisan jariri
- Kwastam ta kama tabar wiwi, man fetur da kuɗinsu ya kai N229m a Ogun
Waɗannan na daga cikin abubuwan da aka ware wa Naira biliyan 47 domin kula da Fadar Shugaban Ƙasa a Kasafin na 2025.
Daga ciki akwai kasafin Naira biliyan 5.5 da aka ware domin aikin kwaskwariman fadar, sai gyaran na’urorin laturoni da sauransu da zai ci Naira biliyan shida.
Naira biliyan 1.8 kuma an ware su ne domin ƙarasa aikin gina ofisoshin masu ba da shawara a fadar shugaban ƙasa.
An kuna ware Naira biliyan 12 domin biyan bashin ayyukan gyara da kamfanin Julius Berger ya yi a Fadar Shugaban Ƙasa.
A ranar Laraba ne dai Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin 2025 na Naira tiriliyan 49, wanda tuni Majalisar Dattawa ta kammal karatu na biyu a kansa.
A halin yanzu kasafin na gaban kwamitin majalisar domin fara aiki a kansa.