✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulani na fuskantar barazana daga sojoji – Badejo

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa Alhaji Bello Abdullahi Badejo, na daya daga cikin ’yan kwamitin sasanta rikici a tsakanin Fulani da manoma…

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa Alhaji Bello Abdullahi Badejo, na daya daga cikin ’yan kwamitin sasanta rikici a tsakanin Fulani da manoma a kasar nan da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya kafa. Aminiya ta zanta da shi lokacin da suka ziyarci Jihar Kaduna don sasanta Fulani da al’ummar Kudancin jihar:

Me za ka ce  game da kashe-kashe da ke faruwa a Najeriya?
Abin da zan ce shi ne dole a kawo karshen wadannan kashe-kashe a kasar nan, musamman rigingimun manoma da makiyaya. Ni Bafulatani ne kuma ban dade da barin yawon kiwo ba, kiwo gadonmu ne, shanu su yi barna a daji gadonmu ne, amma a yanzu babu rikicin manoma da makiyaya. Manoma da makiyaya ba sa rikici domin duk rigingimun da ke faruwa ba asalin manoma ba ne ba kuma ainihin Fulanin da ke kiwo ba ne abin ke faruwa da su.  Zan yi maka misali mun ziyarci Taraba da Binuwai da Nasarawa a karkashin wannan kwamitin tsaro da shugaban ’yan sandan Najeriya ya kafa, mun tarar cewa manoma suna nan suna nomansu, makiyaya na kwarai kuma suna nan suna kiwonsu. Saboda haka akwai sakacin gwamnati na rashin kula da matasa da suka kammala karatunsu amma ba su da aikin yi.
Matashi ya kammala karatu ya dawo gida babu aikin yi, daga nan sai ya zama matsala ga iyayensa. Fulaninmu da rigingimun zaben shekarar 2011 ya shafe su ya sa an salwantar da shanunsu a yanzu babu harkokinyi suna nan suna zaune, gwamnati ba ta yi wani abu a game da wadannan mutane ba.
In babu matasa marasa aikin yi da Fulanin da rigingimu ya sa aka salwantar masu da dukiya, ba za a samu rigingimu ba. Rikicin manoma da makiyaya a wasu wurare ana yin su, amma masu unguwanninsu da ardodinsu suna sasanta su. Wadannan rigingimu na manoma da makiyaya a yanzu wani abu ne na daban wanda siyasa ta shigo cikin lamarin kuma wasu shugabannin da ba su san abin da suke yi ba sun shigo cikin lamarin.
Harkar shugabanci a bangaren Fulani ya lalace, shugabanci a sauran al’ummomi ya lalace, shi ke kara haddasa wadannan rigingimu.
Su wane ne ke haddasa wadannan rigingimu ke nan?
Matasa sun taso watakila babu tarbiyya, kuma suna zaune babu aikin yi, lokacin zabe an dauki Naira dubu daya an ba su sun yi shaye-shayensu. To, zabe ya wuce kuma lokacin zabe bai zo ba, saboda haka suna nan suna zaune.  Fulani kuma da ake musguna mawa suna nan a kasar nan babu iyaka. Babu kuma wanda ya ce wa wadannan Fulani sannu, babu wanda ya san inda irin wadannan Fulani suke zaune. Bafulatani, ka kashe masa uwa da uba da ’yan uwa ya shiga daji, idan babu shanu Bafulatani ba zai zauna a daji ba. Shi ya sa idan rigima ta taso sai dai kaji an ce wai an kashe mutane. Su wa ake kashewa?
Amma ai Fulani ake dora wa laifin wadannan kashe-kashe da ake yi kai kuma ka ce ba su ba ne?
Ana dora mana laifi ne da gangan, yanzu ardon da ke daji zai iya nemanka ya zanta da kai, mutanenmu na da karancin haduwa da mutane kamar ’yan sanda da sojoji da sarakuna, asalin Fulani ba sa iya kaiwa ga wadannan mutane. Kuma wadanda ke tsalle-tsalle a cikin gari suna kiran kansu shugabannin Fulani ba kokari suke su kare mutuncin Fulanin ba, illa kokarin kare abin da su za su samu daga gwamnati. Wani ba za a kira shi taro ba, sai rikici ya taso idan kuma ya halarci taro an dauko kudi an bashi ya shiga mota, ka ga ai ba zai so rikici ya kare ba.
Wace hanya za a bi don magance wannan matsala?
A duk inda ake rikici idan wani yana ganin yana da karfi abokin rikicin yana ganin yana da karfi daga lokacin da aka samu shugabannin kwarai suka ce ya kamata a yafe wa juna to su masu ikirarin karfin babu yadda za su iya domin an riga an karya lagonsu. Kuma ina son ka gane cewa shugaban ’yan sandan Najeriya M.D. Abubakar ne ya kafa wannan kwamiti wanda ina daya daga cikin mambobinsa.
’Yan sanda na da hanyoyi da za su iya magance rikici idan suna so. Ka ga da farko yanzu an dauki matakin fada wa mutane cewa a bar rikici a sasanta. Kuma ai suna iya  kama kowa da kowa amma ai ka ga ba su dauko wannan hanya ba. Shi ya sa nake cewa duk wani abu da ke faruwa idan aka yi kokari aka tsare cikin sauri sai a ga an sami sauki.  Ina tabbatar maka cewa da kafa wannan kwamiti mako biyu ke nan wallahi rayukan da Allah Ya taimaka ba su salwanta ba suna da yawa. Misali a Jihar Binuwai akwai inda Fulani ba sa shiga haka Tibi su ma akwai inda ba sa shiga, amma yanzu abin ya yi sauki. Saboda shugabannin Tibi da na Fulani duk sun yarda babu fada a tsakaninsu.
Kana ganin kwamitin zai taimaka wajen samar da zaman lafiya?
Kwamitin zai taimaka domin ko a yanzu an zauna da shugabannin al’ummar Kudancin Kaduna da sauran shugabannin sauran al’ummomin yankin da shugabannin Fulani, saboda haka nan ba da dadewa ba za a ga wannan abu ya kare. Da zaran an fada wa duniya cewa an sasanta da zarar wani ya ji zai ji dadi a ransa cewa an sasanta.  Ina jin ba a taba yin haka a baya ba, insha Allahu batun zai zo da sauki.
Wasu na ganin kamata ya yi kwamitin naku ya shiga cikin daji domin ganawa da mutanen da ke can maimakon ganawa da shugabanninsu domin ana zargin shugabannin da hura wutar fitinar?
A baya na fada maka cewa akwai wadanda suke cewa su shugabanni ne suke kara rura wutar rikicin.  Amma mu da muke sama ba za mu so a ce kasa ta lalace ba. Akwai wasu mutane da muka fada masu gaskiya inda muka jawo hankulansu game da muhimmancin wannan kwamiti. Ina tabbatar maka cewa zuwan wannan kwamiti kamar mun zo ne muka bude masu ido domin su ci gaba da zama suna tattaunawa a tsakankaninsu.  Akwai bangaren Fulani mutum bakwai su ma ’yan kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU) suna da mutum bakwai da za su rika zama suna fada mana yadda al’amura ke gudana an kuma ba da lambar ’yan sanda idan akwai wata matsala za a sanar don a magance ta cikin gaggawa.
Nan ba da dadewa ba wannan kwamiti zai shiga daji domin ganawa da wadancan Fulani. Mun kuma fada wa duk wanda ka gan shi a wurin taron ya tabbatar da cewa ainihin Fulani ne suka turo shi.  
An zargi sojoji da kashe Fulani a Jihar Nasarawa kwanakin baya, wane mataki za ku dauka?
Fulani na fuskantar barazana daga sojoji, ba a Jihar Nasarawa kadai ba a kusan sassan kasar nan.
Matakin da za mu dauka shi ne wanda ya mutu dai ya rigaya ya mutu, kuma idan aka dubi yanar gizo za a ga hotunan gawarwakin saboda haka mu za mu jira mu ga me hukuma za ta yi. Domin na tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta zura ido tana kallon irin wannan abu na faruwa ba.