A shekaranjiya Laraba kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons ta yi abin kirki bayan ta lallasa takwararta ta Korea Republic da ci 2-0 a ci gaba da fafafatawa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata da yanzu haka yake gudana a Faransa.
A wasan farko Norway ce ta lallasa Najeriya da ci 3-0.
Sai dai yanzu Najeriya ta farfado kuma za ta hadu a wasanta na uku ne da kasar Faransa mai masaukin baki a ranar Litinin.
Kyaftin din kungiyar Asisat Oshola ce ta jefa kwallo ta biyu a ragar Korea Republic yayin da kwallon farko ’yar Korea ce ta ci gidansu (own goal).
Idan ’yan matan suka samu nasara ko kunnen doki a wasansu na gaba, za su haye mataki na gaba. Amma idan suka sake Faransa ta lallasa su, to sai buzunsu, don za su yi ban kwana da gasar tun ba a je ko’ina ba.
Kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu da Kamaru ne suke wakiltar Nahiyar Afirka a wannan gasa.