✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Fiye da Naira biliyan 5 za a ba kasar da ta lashe kofin

Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta bayyana jadawalin kudin da kasashen da ke fafatawa a gasar cin kofin duniya da yanzu haka…

Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta bayyana jadawalin kudin da kasashen da ke fafatawa a gasar cin kofin duniya da yanzu haka yake gudana a Brazil za su samu tun daga matakin farko zuwa na karshe a gasar.
Hukumar ta ce duk kasar da ta lashe kofin za ta samu kason Dala miliyan 35 kwatankwacin Naira biliyan 5 da miliyan 700 yayin da wacce ta zo ta biyu kuma za ta samu kason Dala miliyan 25 kwatankwacin Naira biliyan 4 da miliyhan 100.  Sannan kasar da ta zo ta uku wato (3rd place) za ta tashi da kyautar Dala miliyan 22 kwatankwacin Naira  biliyan 3 da miliyan 608 yayin da ta hudu kuma za ta tashi da Dala miliyan 20 da ya yi daidai da Naira biliyan 3 da miliyan 280.
Sauran kyaututtukan sun hada da Dala miliyan 14 ga kasashen da suka kai matakin kusa da na karshe wato Kwata-Fainal wanda adadin kudin suka kai Naira biliyan 2 da miliyan 296 yayin da kasashen da suka haye zagaye na biyu a gasar, kowannensu zai samu kyautar Dala miliyan 9 wanda ya yi daidai da Naira Biliyan 1 da miliyan 476.
Sannan kasashen da suka fafata a gasar a matakin farko kowannensu ya samu kyautar Dala miliyan 8 wanda ya yi daidai da Naira Biliyan 1 da miliyan 312.
Tun da farko Hukumar ta ce ta rabawa kasashe 32 da suka samu hayewa gasar dala miliyan 1 da rabi kowannensu wanda ya yi daidai da Naira miliyan 246 a matsayin kudin shirye-shiryen halartar gasar.
Don haka za a iya cewa kasar da ta lashe kofin za ta samu adadin fiye da Naira biliyan 20 daga matakin farko zuwa na karshe a gasar.