Hukumar Kula da ’Yan gudun hijira ta Duniya ta yi gargadin karuwar rasa rayuka da aka yi a shekarar bara kusan ninki biyu daga shekarar 2020.
Sama da bakin haure da ’yan gudun hijira da masu neman mafaka 3,000 ne suka mutu ko kuma suka bace a bara a lokacin da suke kokarin shiga Turai ta ketare tekun Mediterrenean da Atlantic, a cewar wani sabon rahoto da Hukumar Kula da ’Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta fitar.
- Gwamnatin Borno za ta kwace kadarorin Majalisar Dinkin Duniya
- Fiye da rabin yara a Ukraine sun koma ’yan gudun hijira – UNICEF
Shabia Mantoo, mai magana da yawun Hukumar Kula da ’Yan gudun hijira ta MDD ne ya bayyana wa wani taron manema labarai hakan a Geneva ranar Juma’a.
Ya ce an bukaci a gaggauta toshe dukkanin hanyoyin da ake samun mace-macen ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka da kuma ‘yan cirani da ke kokarin isa Turai.
Hukumar UNHCR ta fara fitar da kididdigar a shekarar 2019 kuma adadin rayukan da ake rasawa ya karu kowace shekara tun daga lokacin.
“Muna ganin karuwar rasa rayukan kuma wannan abin ban tsoro ne,” in ji Mantoo.
Daga cikin kididdigar shekarar 2021, mutum 1,924 ne aka bayar da rahoton sun mutu ko kuma sun bace a kan titin Tsakiya da yYammacin Bahar Rum, a cewar rahoton na UNHCR.
An ba da rahoton wasu karin 1,153 sun mutu ko kuma sun bace a hanyar tekun Arewa maso Yammacin Afirka zuwa tsibirin Canary.
“Yawancin mashigar tekun an yi su ne a cikin cunkoso, marasa inganci, kwale-kwalen da suke wucewa suna iya nutsewa – da yawa daga cikinsu sun kife ne, lamarin da ya kai ga asarar rayuka,” in ji Hukumar.
Wadanda suka mutu da bacewar sun fito ne daga kasashe daban-daban na Arewaci da Kudu da hamadar Sahara da suka hada da: Tunisia da Morocco da Mali da Guinea da Eritrea da Egypt da Ivory Coast da Senegal, da Iran da Syria da Afghanistan, in ji Mantoo.
Kididdigar rasuwar ba ta hada da wadanda suka bata ta hanyar bi ta kasa ba, kamar ta hamadar Sahara da ake hukuntawa ko kuma wadanda aka rasa a cibiyoyin tsare masu fasa kwauri inda wadanda suka tsira suka ba da rahoton cin zarafi da auren dole da aikatau.