Fiye da matasa dubu biyu ne kungiyar Koyar da Sana’o’i ta Gwamnatin Jihar Nasarawa da ke garin Lafiya, ta yaye ta kuma samar musu da tallafin kayayyakin aiki tun bayan kafa kungiyar shekara hudu da suka wuce.
Shugaban kungiyar Injiniya Ibrahim Adamu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu, game da harkokin kungiyar. Ya ce kungiyar tana samar wa matasa maza da mata daga ciki da wajen jihar sana’oi daban-daban da suka hada da aikin walda da gine-gine da kafinta da gyaran gashin kai da saka da dinki da dai sauransu, wanda a halin yanzu acewarsa wadanda kungiyar ta yaye ta samar musu da tallafin kayayyakin aiki da suke basu damar fara nasu sana’o’i don dogara da kansu.
Ya ce kungiyar kasancewa ta gwamnati ce tana daukar matasa don koya musu wadannan sana’o’i kyauta ba tare da sun biyan sisin-kwabo ba, kamar yadda a cewarsa wasu kungiyoyi irin wannan a wasu jihohin kasar nan ke yi. Ya kara da cewa kungiyar tana biyan kowanna dalibinta naira dubu uku a kowane karshen wata a matsayin alawus don tallafa musu su wajen biyan bukatunsu na yau da kullum.
Daga nan ya shawarci iyaye da su turo ’ya’yansu kungiyar don koyon wadannan sana’o’i donsu dogara da kansu maimakon su rika jiran aikin gwamnati da a cewarsa ba kowa ne ke samu ba. Har ila yau, ya jinjina wa gwamnatin Umaru Tanko Almakura dangane da kirkiro da kungiyar da a cewarsa tana rage zaman banza a tsakanin matasa. Ya kuma mika rokonsa ga gwamnan da ya samar musu da isassun kayayyakin aiki don inganta ayyukansu kasancewa suna samun karin dalibai da ke neman shiga kungiyar don koyon sana’o’i.
Game da nasarar da Gwamna Almakura ya sake samu na zabansa a matsayin gwamnan jihar karo na biyu kuwa. Injiniya Ibrahim Adamu ya bayyana cewa nasarar gwamnan bai zame masa abin mamaki ba, kasancewarsa mai kishin ci gaban jihar a zahiri. Daga nan ya ba da tabbacin cewa a cikin shekaru hudu na wa’adinsa, jihar za ta samu ci gaba a kowanna bangare fiye da yadda yake a da.