Fitattun mutane da dama a sassan duniya sun tsinci kansu a cikin tsaka mai wuya saboda karya dokar cutar COVID-19 da suka yi.
A baya-bayan nan ne dai Fira Ministan Birtaniya da kansa ya amsa cewa ya karya dokar ya kuma ba da hakuri, amma wasu suka ce allambaran, sai dai ya sauka daga mukaminsa.
- Abin da ya sa mahauta suka daina tallar nama
- Fira Ministan Birtaniya ya nemi afuwa kan zuwansa casun COVID-19
Mayan mutan da suka hada da sarakai da manyan ’yan siyasa da tarurarin shirye-shiryen talabijin da ’yan wasan motsa jiki da dama sun shiga irin wannan tsaka mai wuya saboda karya dokar kariyar cutar.
Daga cikinsu har da Fira Minsitan Birntaniya, Boris Johnson da ministocinsa da shahararren dan wasan kwallon Tennis, Novak Djokovic da tauraruwar shirin talabijin, Kim Kardashian da ’yan gidan sarautar Dutch da irin hakan ta ritsa da su.
Ga wasu daga cikinsu:
– Fadar Gwamnatin Birtaniya –
Gwamnatin Tsohon Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson ta shiga tsaka mai wuya bayan babban mashawarcinsa, Dominic Cummings, ya karya dokar kullen COVID-19 a watan Mayun 2020, inda ya yi wata doguwar tafiya domin zuwa wurin iyayensa a lokacin.
Daga baya kuma ya sanar cewa ya yi wata tafiyar domin “duba lafiyar idonsa” kafin daga bisani a hura masa wutar da ta sa shi yin murabus daga mukaminsa.
Dambarwar ta Cummings ita ce mafi tsawo da ta shafi karya dokar COVID-19 da ta dabaibaye gwamnatin Mista Johnson.
– Ministan Lafiyar Birtaniya –
Ministan Lafiyan Birtaniya, Matt Hancock, ya sauka daga mukaminsa kan karya dokar COVID-19 din da ya kafa, bayan bullar hotonsa ya rungume budurwarsa, wadda ma’aikaciya ce a ma’aiaktarsa a watan Yunin 2020.
– Boris Johnson da mahaifinsa –
Shi kan shi Boris Johnson ya dade cikin tsaka mai wuya bayan bayyanar hotonsa a wurin wani shagali da aka shira a fadarsa sabanin dokar COVID-19.
A ranar Laraba ya bayar da hakuri han halatar wani shagali da ya yi a farko-farkon kullen 2020, a daidai lokacin da wasu ke neman ya sauka daga mukaminsa.
Shi ma mahaifinsa Stanley, an gano shi a jirgi a kan hanyarsa ta zuwa gidansa da ke kasar Girka, ba tare da ya sanya takunkumi, da sunan zai je gidan ne domin tabbatar da babu “COVID-19”, alhali an takaita tafiye-tafiyen da ba su zama dole ba.
– Shugaban Afirka ta Kudu –
Shi ma Shguaban Kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya karya dokar bayar da tazarae COVID-19, inda ya dauki hoton ‘selfie’ da wasu mata biyu da suka bukaci hakan daga gare shi a watan Mayun 2020.
A bidiyon nasa da ya karade gari, an ji shi yana dariya yana ce musu, “Ku zo mu dauki hoton kafin a tsare mu.”
Sai dai ba a tsare shi ba, amma bidiyon nasa ya karade kafafen zumunta, inda ya ja masa suka sosai.
– Minista a gidan casu –
Minista a Ma’aikatar Lafiyar kasar Paraguay, Juan Carlos Portillo, ya yi murabus bayan an yada bidiyonsa a wani gidan casu da ya laharta a watan Yunin 2020, jim kadan bayan ya taimaka an sanya dokar COVID-19 a kasarsa.
– Gidan Sarautar Dutch –
A watan jiya, iyalan gidan Sarautar Dutch sun nemi afuwa bayan da suka gayyaji wasu mutum 21 domin halartar bikin cika shekara 18 na Sarauniya Mai Jiran Gado, Gimbiya Amalia, alhali dokar ta takaita yawan taruwar mutane zuwa mutum hudu kacal.
Hasali ma, an sha ganin Sarki Willem-Alexander yana karya dokar bayar da tazara, yana yin musafaha da mutane, iyalan gidan kuma suna zuwa hutu a kasar Girka a lokacin kullen cutar.
– Kim Kardashian –
Tauraruwar shirin talabijin, Kim Kardashian, ta sha caccaka a watan Oktoban 2020 bayan ta shirya casun bikin cikarta shekara 40 a wani tsibiri da ta mallaka.
Fitar hotunan mahalarta shagalin babu takunkumi a fuskokinsu ya ja wa tauraruwar suka sosai.
– Firam Ministan Poland a gidan abinci –
Fira Ministan kasar Poland, Mateusz Morawiecki, ya nemi afuwa a watan Mayun 2020 bayan da ya dauki hoto da ma’aikatan wani gidan abinci, alhali yana umartar mutane cewa ko abinci za su ci, ta tabbata da danginsu na kusa ne ba taer da baki ba.
– Kwamishinan Kasuwancin EU –
A watan Agusatan 2020, Kwamishinan Kasuwancin Tarayyar Turai, Phil Hogan, ya yi murabus bayan ya sha matsin lamba tare da wasu manyan ’yan siyasa biyu na kasar Ireland a wasan golf da majalisar dokokin kasar ta shirya.
Mutum 80 suka laharci wurin alhali a lokacin mutum shida aka amince su yi taro a cikin gini mai rufi.
Ita ma Shugabar Hukumar Yawon Bude Ido ta kasar, Catherine Martin, an matsa mata, har ta yi murabus, saboda ta tafi hutu kasar Italiya bayan an umarci mutane da su yi hutunsu a cikin kasar.
– Gwmanan California –
Bayan shan matsin lamba, Gwamnan Jihar California ta kasar Amurka, Gavin Newsom, ya amsa cewa ya tafka “mummunan kuskure” a watan Nuwamban 2020 inda ya halarci taron bikin zagayowar ranar haiwuwar wani abokinsa a lokacin da aka samu karuwar masu kamuwa da COVID-19.