✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FITATTUN MATA

Hajiya Zainab Buba Galadima: Burina in zama abar jingina ga mata Zainab ‘yar Buba Galadima ce, Sakataren Jam’iyyar CPC na kasa, kuma ita ce kansilar…

Hajiya Zainab Buba Galadima: Burina in zama abar jingina ga mata

Zainab ‘yar Buba Galadima ce, Sakataren Jam’iyyar CPC na kasa, kuma ita ce kansilar Wuse 11 a Birnin Tarayya Abuja. Ta yi digiri a fannin lissafi. Ta ce mahaifinta ne ya ba  ta shawarar shiga siyasa, ta kuma ce burinta ta zama abar jingina ga mata. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Tarihin rayuwarta
Zainab: Sunana  Zainab Buba Galadima, an haife ni a garin Maiduguri, mahaifina shi ne Injiniya Buba Galadima Sakataren Jam’iyar CPC na kasa; mahaifiyata kuma ita ce Hajiya Fanna Buba Galadima. Na yi karatun firamare a Maiduguri Primary School, daga nan sai na sakandare a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta ‘yan mata (FGGC) da ke Bakori a Jihar Katsina. Bayan nan sai na wuce Ingila a inda na samu takardar gaba da sakandare a makarantar Paddocks. Ingila. Na je wata makaranta a Birtaniya ta kasuwanci da kuma makarantar Webstar. Na yi karatun digiri dina a sashen lissafi, sannan na yi digiri-na-biyu daban-daban har uku duk a makarantar Webster. Na samu wadannan digirori-na-biyu a fannin sadarwa da gudanarwa da kuma kimiyya da kere-kere. Nan gaba kadan zan zama kwararriyar mai lissafi. Na yi hidimar kasa bara. Sannan kuma na tsaya takarar kansila a Wuse11 a ranar 16 ga watan Mayu 2013. Allah Ya ba ni sa’a na ci zabe, kuma makon jiya aka rantsar da mu. Ni ce ‘ya ta farko a gidanmu, ina da kanne 11; maza 8 ke bi na sannan mata uku, a watan Janairu da ya wuce aka yi mini aure.
Wane ne Ibrahim?
Ibrahim: Sunana Dauda Yusuf Ibrahim, ni mutumin Jihar Jigawa ne, kuma na yi karatu a makarantar Command Children School Jaji, na yi karatun firamare a Kano, kuma na yi karatun sakandare a Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) duk a Kano. Daga nan na wuce zuwa jami’ar Obafemi Awolowa ta Ile-ife inda na yi digirina, sannan kuma na yi babban digirina a Jami’ar Bayero ta Kano. Na fara aiki da Kamfanin mai na NNPC, daga nan na yi aiki da Kamfanin jirgin sama na British Airways, kafin na yi aiki da wani kamfanin Turawa da ke harkar mai. Daga nan kuma na bar su na fara tawa sana’ar.
A gidanmu, mu takwas ne, ina da yayye biyu da kanne biyar. Ni ne namiji babba, kuma tun da Allah Ya yi wa mahaifinmu rasuwa nake tafiyar da al’amarin gida.
Yadda na hadu da Zainab
Ibrahim: Mun hadu da ita ne a wajen wanke mota ne, naje wanke motata, sai Alllah Ya sa ta kawo motar gidansu wanki. Daga nan, na tsaya ina kallon su har suka ajiye motar suka tafi. Sai na ba da katina na ce don Allah idan ta zo a ba ta, kuma in da hali a gaya mata ta kirani. Daga baya ta kira ni ta yi min kwatancen gidansu, na je na same ta. Muka fara waya, har abin ya zo ya yiwu. Yau shekaru shida ke nan da haduwarmu.
Halayen Zainab da suke burge ni
Ibrahim:Tana da kwazo, kuma yana cikin abinda yasa na bada katina akai mata kenan. A yanayin yadda ta ajiye mota, da yadda ta rike kanta. Kuma duk abinda take  yi, tanayin iya karfinta. Yana cikin abubuwan da na gani kuma nace zata iya rike kanta.
Halayen Ibrahim da ke burge ni
Zainab: Mutum ne mai gaskiya, kuma komai zai yi yana yin shi tsakaninsa da Allah. Idan mutum na da irin wadannan halayen mutumin kirki ne.
Abubuwan da ba zan manta da su ba a lokacin da nake karama
Zainab: Gaskiya dai na girma a cikin maza, akodayaushe muna cikin neman tsokana cikin unguwa; da su muke hawa keke. Akwai kawayena wadanda muka tashi tare tun muna shekara takwas su ne kawayena har yanzu, kuma in na tuna yadda muka tashi tare a Maiduguri, yadda zaman lafiya yake, yadda muke walawarmu a matsayinmu na Manyan Gobe, amma ga shi kuma yanzu ba ka isa ka samu irin wannan walwalar ba. Yana cikin daya daga abubuwan da nake tunawa. Ga shi kuma idan dare ya yi a lokacin a Maiduguri, mukan fita wasa, ba zan manta ba akan fita gada amma yanzu kuma babu wannan damar. Wannan yana cikin daya daga abubuwan da idan na zauna na ke tunawa.
Iyayena
Zainab: Kowanne daga cikin mahaifana akwai irin shakuwar da na yi da shi. Kamar mahaifina, tunaninmu halinmu daya da shi. Maihaifiyata kuma tana taimaka mini wajen ba ni shawarwari nagartattu. Ta koya mini girki da kuma iya ado da tsafta. Shi kuma mahaifina, yakan ba ni shawara a harkar siyasa da kuma karatuna. Ban zauna da mahaifana sosai ba domin na yi shekaru 13 a kasar Ingila, rayuwata irin ta turawa ce, don nakan yi abubuwa da kaina.

Taimakon iyayena a wajen gudanar da karatuna
Zainab: A gaskiya iyayena sun yi kokari sosai, kasancewar babu abin da zan iya cewa a yanzu sai dai na ce musu Allah Ya saka musu da alheri. Sun tsaya a kan kafafunsu don in samu karatu mai inganci. Mahaifiyata kamar malama take addu’a ba ta tsinkewa a bakinta. Mahaifina kuma, idan akwai bukatar wani abu yakan taimaka sosai. Kuma yakan ba ni shawara ta hanyar da za ta fi mini sauki wajen gudanar da al’amuran rayuwa.
Yadda na shiga siyasa
Zainab: A gaskiya, ni ma abin ya zo mini kamar da wasa. Rannan ina zaune a gida ina kallo sai mahaifina ya ce mini, “da wannan zaman kashe zanin da kike yi ba gara kin shiga siyasa ba?” Sai na yi na’am da shawararsa. Ga shi kuma a lokacin ba ni da ko dubu 20 na kaina. Amma da taimako Allah, sannan da na iyaye da abokan arziki Allah Ya ba ni sa’a na ci zabe.

Yadda nake son taimakawa mata
Zainab:A matsayina ta kansilar Wuse 11, akwai hanyoyi masu yawa da nake son taimaka wa mata, kamar ta fannin sana’a da aikin hannu, ba dole sai dinki ba. Ina son mata su samu ilimin nau’urar kwamfyuta don gudanar da harkokinsu. Domin duniyar ta dunkule ta zama daya. Muna son mu fara wannan, akwai kuma wadanda ba su je makaranta ba zan nema musu jari, dangane da lafiya, muna kokarin bude wani fili na ba mata masu juna biyu shawarwari don kulawa da kansu da kuma irin abincin da za su ci. Muna so mu wayar wa mata kai a kan abubuwan da ya kamata su yi idan suna da juna biyu da kuma bayan sun haihu. Yana daya daga cikin abubuwan na ke son yi. Burina a ce na zama abar jinginar mata.
Burina
Zainab: Ba ni da wani buri. Duk abin da Allah Ya nufe ni da samu zan same shi, idan kuma ban same shi ba ba na tayar da hankalina, domin ni Musulma ce ina imani da kaddara ta alkhairi ko ta sharri. Ina son kuma in gama da abin da ke gabana a yanzu. Nauyi ya karu a kaina, don haka nake son gamawa da abin da yake gabana a yanzu domin sanin irin rikon da na yi kafin komai. Ni ma ina son in mallaki abin kaina. Kamar ta hanyar kasuwanci don rufa wa kaina asiri. Domin mukamin siyasa na lokaci kadan ne daga ya kare sai a rasa madafa.
kalubalen da na taba fuskanta a hanyar karatuna
Zainab: Babban kalubalen da na fuskanta shi ne, a lokacin da nake karatun digiri-na-biyu na hada su biyu. Gaskiya na sha wahala sosai, kuma in kai kadai ne a wuri kewar gida na sa ka dan yi baya a karatu, amma da addu’a na samu na gama, saboda idan ka yi abu mai kyau ka yi wa kanka, haka idan ba ka yi mai kyau ba ma ka yi wa kanka. Karatu ba abu ne mai sauki ba sai mutum ya dage don cim ma burinsa.
Nasara
Nasara wata abu ce wadda idan mutum ya yi Allah zai ba shi sa’a. Ba wai kida ba, kuma duk abin da kake yi idan kana jin dadinsa, to ya kamata ka ci gaba. Duk abin da nake yi har ya zamana ina jin dadin yinsa, sai na samu karfin gwiwa, kuma ina taba rayuwar mutane ta hanyar taimakawa jama’a, wannan ce ma’anar tawa nasarar.
Wurin da na fi sha’awa zuwa hutu
Ina son zuwa Ummra da kuma aikin Hajji. Amma ina son zuwa kasar Faransa musamman Paris don birni ne wanda ke da kayan tarihi, wanda in ka ga abubuwa za ka so ka san me nene don karin ilimi.
Abin da nake son a tunani da shi
Ina son a tunani a matsayin wadda ta tsaya a kan gaskiya, ba kan karya ba. Ya zama duk abin da na fada shi zan aikata.