✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitar da doya ƙasashen Turai: Rashin shigar da masana ya sa aka samu matsala – dandanma

Alhaji Muhammadu Ɗandanma Yaro, shi ne Shugaban kungiyar Masu Hada-hadar Doya ta Shukura na kasa, tsohon ɗan kasuwane da ya shafe sama da shekaru 38…

Alhaji Muhammadu Ɗandanma Yaro, shi ne Shugaban kungiyar Masu Hada-hadar Doya ta Shukura na kasa, tsohon ɗan kasuwane da ya shafe sama da shekaru 38 a harkar kasuwancin doya, kana kuma ɗaya daga cikin shugabannin ’yan Arewa a jam’iyar APC. A zantawarsa da Aminiya a wannan makon, dandanma ya bayyana dalilan da suka sanya shirin gwamnatin tarayya na fitar da doya ƙasashen turai ya gamu da cikas, da kuma hanyoyin da ya kamata abi don ganin an inganta shirin anan gaba.

 

Aminiya: Zamu so ka gabatar da kanka a takaice. 

Muhammadu Ɗandanma:  Sunana Alhaji Muhammadu Ɗandanma Yaro, Shugaban kungiyar ‘Yan kasuwa masu hada-hadar doya ta Shukrah dake kasuwar Mil 12 a nan Legas. 

Aminiya: Ko ya kake kallon shirin gwamnatin tarayya na safarar kasuwancin doya zuwa kasashen Turai? 

Muhammadu Ɗandanma: Wannan al’amari na kasuwancin doya a ƙasashen waje mu ma mun ji ne wai-wai kawai, a matsayin mu na shugabannin na ƙasa a wannan fanni, don muna cikin wannan harka ne tun lokacin da ake sayar da ƙwaryar doya naira 30 yanzu ko ta kai dubu 80 zuwa dubu 100. Yau sama da shekara 38 kuma har yanzu cinkinta mu ke nan, amma a lokacin da wannan lamari na gwamnati ya taso ba a gayyace mu ba, mun dai ji labarin za a kai doya ƙasar waje, sai ga shi an yi abin kunya da wannan azarbabin na fita da doyar daga nan zuwa ƙasar waje har ta lalace, hakika wannan lamari bai yi mana daɗi ba ko kadan. 

Aminiya: A matsayinka na kwararre a wannan harka, me kake ganin ya haddasa lalacewar doyar? 

Muhammadu Ɗandanma: Babban abu dais hi ne ba a nemi waɗanda suka san sirrin harkar bat un da farko, domin doya suna ta tara, wani da ya ji an ce doya, ya ɗauka doya kawai, a’a, doya ta kasu kashi da yawa, akwai ɗan Onicha akwai muyi-muyi wato gambari, akwai doya laushi da gambur da Afur, akwai doya Fefa da anta da Kwankwaso da su akurki, doya na nan kala-kala. To daga ciki akwai wacce ya kamata a fitar ƙasar turai, wacce za ta jure dukkan wahala, akwai agumaka wacce ake kawo wa daga Nasarawa, akwai wacce ba ta jure wahala da ta yi kwana ɗaya biyu uku sai ta lalace, akwai wacce in an yanka sai ta yi jah, wata ko fara zaka ganta. To matsalar da gwamnatin ta samu shi ne waɗanda suka san harkar a takarda kawai ta gayyata, sannan mu da muka santa a aikace ba a shigar da mu ba, don haka in ba gyara aka yi ba, za a cigaba da samun matsala, don haka shawara ta anan it ace, a nemi waɗanda suka san harkar da abin da ta kunsa, muddin ana son shirin ya kai ga nasara, idan an yi haka ba za a sake jin kunya a kasuwannin duniya ba da yardar Allah. 

Aminiya: Wani tasiri kake ganin wannan shiri zai yi ga masu noman doya da ’yan kasuwan ta? 

 

Muhammadu Ɗandanma: Ai wannan abu ne na cigaba ƙwarai, domin akwai manoman ta sossai a ƙasar nan da kuma ‘yan kasuwar ta, sai dai a yanzu ba da su ake damawa ba a shirin, abin da ya kamata ayi shi ne a sanya manomanta da ‘yan kasuwa da suka san harkar, idan an yi haka shi ne kowa zai amfana. Sannan kamar yadda muka ga wannan gwamnati ta himmatu kan sha’anin noma a kasar nan, to muddin an bi hanyoyin da suka kamata, to Najeriya za ta zama sahun gaba a noma da kasuwancin kayan abinci a duniya ba ma a Afirka ba.