Fitaccen mawakin nan wanda ya yi tashe wajen waka da kada jita, Majekodunmi Fasheke, wanda aka fi sani da Majek Fashek ya rasu.
Manajansa, Omenka Uzoma ne ya tabbatar da rasuwar mawakin a shafinsa na Instagram a safiyar yau Talata.
“A yau ina ta samun kiraye-kiraye ta waya. To da gaske ne, lallai fitaccen mawakin Afirka na daya ya rasu. Za mu rika tuna shi da nasarorinsa da iyalansa. Duk abin da iyalansa suka yanke, za mu sanar da jama’a.”
A haifi Majek ne a birnin Benin na Jihar Edo, kuma ya rasu yana da shekara 57 a wani asibiti a birnin New York na kasar Amurka.
A shekarun 80s ne tauraron Majek Fashek ya fara haskawa bayan ya saki wakarsa ta Send Down the Rain.
Kundin wakar ya lashe kyautar kundin waka na shekarar ita kuma wakar ta samu kyautar wakar shekara, sannan aka ba Majek Fashek kyautar mawakin jita na shekarar.
Mawakin ya dan taba shiga harkar fim a tsakanin shekarar 2010 zuwa da 2012. Sannan a shekarar 2016 ya yi wakar We are not afraid.
A shekarar 2015 ce ya talauce da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi, har sai da aka kai shi gidan gyara tunani bayan ya nemi taimako a kafafen sadarwa.
Majek Fashek ya yi fama da matsananciyar jinya a bara. Rashin kudi ya tilasta masa zama a Ingila babu kudin zuwa asibiti babu na dawowa gida. Daga karshe fitaccen dan kasuwa Femi Otedola ya taimaka masa da kudin asibiti.
Mamacin ya auri Rita Fashek wadda ta haifa masa ’ya’ya hudu, amma sun rabu kafin rasuwarsa.