✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ICPC ta tsare D’banj kan kudin N-Power

ICPC ta tsare D'banj, ne bisa zargin karkatar da kudaden shirin tallafin matasa na N-Power

Hukumar Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC) ta tsare fitaccen mawakin Najeriya, Oladapo Daniel Oyebanjo, wanda aka fi sani da  D’banj.

Rahotanni sun nuna a ranar Talata ICPC ta tsare D’banj, domin bincikar sa, bisa zargin karkatar da kudaden shirin tallafin matasa na N-Power.

Rahotanni sun nuna an ga fitaccen lauyan kare hakkin dan Adam, Pelumi Olajengbesi a ofishin ICPC da taek tsare da mawakin.

Wasu majiyoyi sun ce Pelumi Olajengbesi lauya ne ga D’banj, wanda ake wa lakabi da The Koko Master.

%d bloggers like this: