Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan gaskiya.
Almajiransa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a gidansa da ke Bauchi inda za a yi jana’izarsa a safiyar wannan Juma’ar.
Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman magani a ƙasashen Masar da Saudiyya.
Fitowarsa ta ƙarshe ita ce ranar Idin ƙaramar Sallah da ta gabata, inda ya yi huɗuba kan muhimmanci haɗin kai a tsakanin musulmi.