✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fitaccen jarumi Kasimu Yero ya rasu

Allah ya yi wa fitaccen jarumin funafinan Hausa, Alhaji Kasimu Yero rasuwa. Kasimu Yero ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa da…

Allah ya yi wa fitaccen jarumin funafinan Hausa, Alhaji Kasimu Yero rasuwa.
Kasimu Yero ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke Jihar Kaduna bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Dansa mai suna Mansur Yero shi ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa ga wakilin Aminiya.
An binne shi a Magajin Gari da ke garin Zariya a Jihar Kaduna da misalin karfe biyu na rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.