Niyi Bandele, daya daga cikin fitattun daraktocin fina-finan masana’antar Kudancin Najeriya ta Nollywood, ya rasu.
Daraktan ya rasu ne a ranar Litinin yana dan shekara 54 a duniya, a wata sanarwa da ‘yarsa Temi Bandele ta fitar.
- Majalisar Dinkin Duniya ta kira taron gaggawa kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa
- An kira ni a waya kusan sau 1,000 don tabbatar da labarin mutuwata – Kabiru Nakwango
Tauraron marigayin ya haska ne a lokacin da ya bayar da umarnin fim din littafin Chimamanda Adichie mai suna ‘Half of a Yellow Sun’ a shekarar 2013.
Amma kafin nan, ya yi wasu fina-finan da yawa, kamar su ‘Fifity’ wanda ke nuna rayuwar matan Africa a wannan zamani, wanda aka nuna a bikin baje kolin fina-finai na birnin Landan a shekarar 2015.
Wasu karin fina-finan da ya yi sun hada da ‘Blood Sisters’ mai dogon zango da ya yi wa kamfanin Netfilx.
‘Yan uwa da abokansa na kusa, da kuma sauran wadanda suka yi aiki tare tuni suka fara juyayin rashinsa.
Suna haka ne ta aika sakonnin ta’aziyya da kuma irin kewa da suke yi na rashinsa da kuma yabon halayensa, musamman a shafukan sada zumunta.