✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiyar Ingila: Gobe Man City take sa ran daga kofi

A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila, gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a shawo ta a tsakanin manyan kungiyoyin…

A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila, gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a shawo ta a tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu da ke birnin Manchester na Ingila, kuma idan City ta samu nasara zai zamo ta lashe gasar ta bana ke nan. Kulob din biyu da za su gwada kwanjin su ne Manchester City da Manchester United. Masu sha’awar kwallon kafa a Najeriya musamman a Arewa suna kiran kungiyoyin biyu da Manchester ta birni (City) da kuma ta kauye (United).

Wasan zai gudana ne da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya, inda ake sa ran gidajen kallon kwallo za su cika don ganin yadda wasan zai kaya.

Wasan zai yi zafi sosai domin idan City ta doke United, za ta zama zakara tare da ta ba United da ke matsayi na biyu tazarar maki 19 kuma saura wasa 6 a kammala gasar. Don haka ko da United ta samu nasara a sauran wasannin ba za ta iya kamo City ba, tunda wasannin da suka rage zai zama maki 18 ne. Amma idan United ta samu nasara a kan City ko suka yi kunnen doki, to sai City ta jira wasa na gaba kafin ta san matsayinta kan lashe kofin.

Kamar yadda masana harkar kwallo suka yi hasashe, Kocin City, Pep Guardiola zai yi duk mai yiwuwa wajen doke kulob din United domin ya kafa tarihi a gasar ta Firimiya, yayin da Koci Jose Mourinho na Manchester United zai turje don ganin City ba ta samu nasara a kansa gida da waje ba.

Kawo yanzu dai City ce ke saman tebur a gasar da maki 84 yayin da United ke matsayi na biyu da maki 68 sai Liberpool ta uku da maki 66 sai Tottenham ta hudu da maki 64.