✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fira Ministan Rasha ya kamu da Coronavirus

Fira Ministan Rasha Mikhail Mishustin ya kamu da cutar coronavirus. Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya…

Fira Ministan Rasha Mikhail Mishustin ya kamu da cutar coronavirus.

Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin da yammacin ranar Alhamis.

A wani rahoto da kafar watsa labarai ta RT ta wallafa ta ruwaito  cewa, a halin yanzu mataimakin Firayi Ministan shi ne wanda zai ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati, kafin Firayi Ministan ya murmure.

Mista Mishustin, ya karbi sakamakon gwajin da aka yi masa ne a lokacin yana tsaka da aiki.

Mishustin shi ne Shugaba na biyu da ya kamu da wannan annoba a cikin manyan shugabnin duniya bayan Fira Ministan Birtaniya Mista Boris Johnson.

Mista Mishustin, ya shaidawa manema labarai cewa, “dole ne a yanzu na killace kaina domin kada na yada wannan cuta ga abokan aikina, kamar yadda likitoci suka bani shawara. Abin da ya same ka gobe yana iya shafar wani.”

Shugaba Putin, ya bayyana cewa jami’an gwamnatinsa suma suna cikin hadarin kamuwa da cutar ta Covid-19.

Firayi Ministan ya shaidawa shugaba Putin, cewa zai ci gaba ta tuntubar abokan aikin sa akai-akai ta hanyar waya da kuma ta kafar na’urar hoton bidiyo.