✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Finland za ta shiga NATO saboda firgita da mamayar Rasha a Ukraine

Rasha ta ce wannan barazana ce a gareta kuma za ta mayar da martani.

Finland ta tabbatar da niyyar shiga Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO/OTAN ba tare da bata lokaci ba, inda ake sa ran kasar Sweden ta biyo baya, saboda firgita da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.

A ranar Alhamis ce kasar Finland ta tabbatar da niyyar shiga Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO/OTAN cikin gaggawa, inda ake sa ran kasar Sweden za ta bi sahu.

Kasashen biyu sun kasance ’yan ba ruwanmu kan shiga wani bangare na kawance soja tun bayan yakin duniya na biyu, sakamakon makwabtaka da tsohuwar Tarayyar Soviet.

Amma komai ya sauya sakamakon kutsen da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya kaddamar a kan kasar Ukraine.

Tuni mahukuntan Rasha suka ce matakin shiga Kungiyar Kawancen Tsaron ga kasashen biyu na Finland da Sweden na zama barazana ga kasar ta Rasha kuma za ta mayar da martani, sai dai bata tantance irin matakin da za ta dauka ba.