✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA za ta ba golan Najeriya diyyar Naira miliyan 8

Rahotannin da ke fitowa daga Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) sun ce hukumar za ta ba golan Najeriya Frances Uzoho diyyar Yuro dubu 20…

Rahotannin da ke fitowa daga Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) sun ce hukumar za ta ba golan Najeriya Frances Uzoho diyyar Yuro dubu 20 da 548 (wanda ya yi daidai da Naira miliyan 8 da dubu 239 da 240) saboda raunin da ya ji a wasan da Super Eagles ta yi da kasar Brazil a ranar Lahadin da ta wuce.

Golan ya ji rauni ne bayan sun yi arangama da dan kwallon Brazil Casemiro a wasan da Super Eagles da Brazil da aka tashi 1-1.

Sabuwar dokar da FIFA ta fitar ta nuna duk dan kwallon da ya ji rauni a  wasannin sada zumunta ita za ta dauki nauyin biyan diyya ko jinya har sai ya warke.

Dokar za ta shafi Frances Uzoho golan Najeriya da Neymar Jnr na Brazil da duk ’yan kwallon da suka ji rauni a yayin wasannin sada zumuntar da aka yi a makon jiya.

Sai dai dokar ta nuna hukumar za ta biya ne ga ’yan kwallon da za su shafe akalla mako hudu suna jinya.

Uzoho dai zai shafe wata shida yana jinya saboda raunin da ya samu a wasan, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.