✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FIFA ta hukunta Najeriya kan hargitsin da aka tayar a filin wasa na Abuja

An kuma haramta wa ’yan kallo shiga fili a wasanta na gaba da za ta fafata a gida.

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta dauki matakan hukunta Najeriya kan abin da ta kira rashi da’a da magoya bayan tawagar kwallon kafar kasar suka nuna bayan an tashi wasan neman shiga gasar Kofin Duniya da aka fafata tsakanin tawagarta ta Super Eagles da tawagar Black Stars ta Ghana.

Aminiya ta ruwato cewa, magoyan bayan Super Eagles sun tayar da hargitsi a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, inda suka rika kokarin lalata duk wani abu da suka ci karo da shi domin huce takaicin rashin samun damar yankar tikitin zuwa gasar Cin Kofin Duniya da za a fafata bana a Qatar.

Daga cikin matakan ladabtarwa da FIFA ta dauka kan Najeriya sun hada da tarar Dalar Amurka 154,128.75 da kuma haramta wa ’yan kallo shiga fili a wasanta na gaba da za ta fafata a gida.

A ranar 29 ga watan Maris da ya gabata ne Najeriya ta karbi bakuncin tawagar Black Stars a Ghana a zagaye na biyu na neman gurbin zuwa gasar Cin Kofin Duniya, wanda aka tashi 1-1 biyo bayan canjaras da aka yi mara ci yayin da tawagar Najeriyar ta je bakunta Ghana kafin sa.

Duk da cewa shi ma wasan na biyu an tashi kunnen doki, amma hakan bai hana Ghana samun damar yankar tikitin gasar kwallon kafar mafi daraja a sakamakon kwallo daya tilo da ta jefa a ragar Najeriya har gida.

Ya zuwa yanzu dai Hukumar Kwallon Kafar Naeriya NFF ba ta ce uffan a kan hukuncin da FIFA ta dauka ba.