✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fetur ya koma Naira 162 a gidajen mai —IPMAN

Dillalan mai sun ce ba su da zabi face sayar da shi a kan N162 domin cike gibi

Kungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu ta kasa (IPMAN) ta umarci ’ya’yanta a yankin Kudu maso Yamma da su sayar da litar mai a kan Naira 162.

Shugaban IPMAN na yankin Kudu maso Yamma, Alhaji Dele Tajudeen a wata hira da ya yi da manema labarai ta waya a Abeokuta, Jihar Ogun, ya ce ’yan kungiayar ba su da zabi face su sayar da litar man a kan Naira 162.

Tajudeen ya ce, wannan ya biyo bayan karin farashi da Gwamnatin Tarayya ta yi a wajen dakon man a defo-defo da ke fadin kasar nan wanda gwamnati ta yanke farashin a kan Naira 151. 56k.

Ya Kara da cewa tun da har gwamnati ta yanke farashin Naira 151.56k, to IMPMAN ba ta da wani zabi face da sayar da shi a kan 162 domin cike gibin da za ta samu.

Tajudeen ya ce, dole ’ya’yan IPMAN su yi lissafin kudin man dizal da za su kona a gidajen mansu kafin su sayar da man ga direbobi.

“Dole sai mun yi lissafin kudin man da mota za ta sha daga defo zuwa inda za a sauke shi da kuma sauran harajin da muke biya ga hukumomi da dama.

“Idan aka yi lissafin kudaden da za a kashe daga inda ake dauko shi har zuwa gidan man da za a sauke zai kai kimanin Naira 160.

“Don haka ne dole farashin da za a sayar a gidan mai ya kai 162; Wannan shi zai ba da dama ga ’ya’ya kungiyarmu su iya biyan kudaden da suke kashewa a kan hanya kafin ya kai ga gidan mai.