Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, wanda ya yi kaurin suna wurin sukar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Fani-Kayode, wanda ya samu rakiyar Shugaban Rikon Jam’iyyar APC na Kasa, Mai Mala Buni a ranar Alhamis.
A jawabinsa, Femi Fani-Kayode ya ce ya koma jam’iyyar APC ne domin hadin kan Najeriya.
Tsohon kakakin na Kwamitin Yakin Neman Zaben Jam’iyyar PDP, ya kuma bayyana cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin wasu gwamnonin PDP uku sun sauya sheka zuwa APC.
Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad, wanda a baya ya sauya sheka daga PDP zuwa APC na daga cikin ’yan rakiyar tsohon ministan, wanda ya ce yana daga cikin mambobin APC na farko
A cewarsa, a halin yanzu yana zawarcin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da Bala Mohammed na Jihar Bauchi da kuma Ifeanyi Uguanyi na Jihar Enugu su sauya sheka zuwa APC.