✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fataucin makamai a jirgin shugaban CAN: ’Yan majalisa sun kaurace wa zama

Fiye da rabin ’yan Majalisar Wakilai ta Tarayya sun fice a fusace daga zauren majalisar a ranar Talatar da ta gabata, bayan da Mataimakin Shugaban…

Fiye da rabin ’yan Majalisar Wakilai ta Tarayya sun fice a fusace daga zauren majalisar a ranar Talatar da ta gabata, bayan da Mataimakin Shugaban Majalisar Mista Emeka Ihedioha ya hana a yi muhawara a kan jirgin Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Fasto Ayo Oreitsejafor da aka kama makare da kudi don sayen makamai a kasar Afirka ta Kudu.
Mista Emeka Ihedioha dai ya yi watsi da shawarar wani dan majalisar ne ta a yi muhawara a kan wannan batu, bisa hujjar cewa batu ne da ya shafi tsaron kasa.
’Yan majalisar da suka fice a fusace sun hada da daukacin wakilan Jam’iyyar APC da wasu daga Jam’iyyarm PDP.
dan Majalisa Abdurrahman Kawu Sumaila na Jam’iyyar APC kuma shugaban marasa rinjaye ne ya gabatar da kudirin neman a binciki fasa-kwaurin Naira biliyan daya da rabi da wasu ’yan Najeriya biyu da wani Bayahude daya suka yi zuwa kasar Afirka ta Kudu a cikin jirgin Shugaban CAN, Fasto Ayo Oritsejifor.
Ya nemi kwamitin tsaro da na sufurin jiragen sama su gudanar da bincike kan lamarin da ya jawo wa kasa abin kunya, domin kauce wa zafafa harkokin siyasa da zubar da mutuncin kasar nan.
To, amma sai Ihedioha ya ce batun ya shafi tsaron kasa, inda ya bukaci a yi kuri’a ta amfani da murya kan a tattauna a kai ko a’a, inda majalisar ta zabi a’a.
Wannan ya fusata wakilan APC da wasu na PDP inda suka kaurace wa zaman majalisar.
Sai dai ’yan majalisar da suka fice daga zauren majalisar sun yi zargin cewa an bai wa wasu takwarorinsu toshiyar baki ta Dala dubu 20 kowanne saboda su danne tattaunawa a kan wannan batu.
Majalisar Dattawa kuwa kwamitinta na tsaro ya fara bincike kan lamarin, inda kwamitin a karkashin Sanata George Thompson Sekibo ya gana da shugabannin sassan soja da mashawarcin Shugaban kasa kan harkokin tsaro a harabar majalisar.
Ya ce, akwai tambayoyi nan da can da suke bin diddiginsu don gano gaskiya kana bin da ya faru.