✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasto ya sha da kyar yana kokarin lalata da matar da yake wa addu’a

Rundunar ‘yan sandan Legas ta ceto wani fasto daga hannun wasu matasa da suka fusata, suka lakada masa dukan kawo wuka bayan da ya yi…

Rundunar ‘yan sandan Legas ta ceto wani fasto daga hannun wasu matasa da suka fusata, suka lakada masa dukan kawo wuka bayan da ya yi yunkurin yin lalata da wata mace da yaje gidanta domin ya yi mata addu’a.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan yankin Ejigbo a Legas suka ceto faston mai suna David Daniel, a hannun wasu matasa da suka lakada masa duka, ya ce ‘yan sanda sun kuma tsare faston akan zargin yunkurin yin lalata da matar da yaje gidanta domin yi mata addu’a.

Ya ce, da fari dai faston mai shekaru 41 ya ziyarci matar mai suna Joy Muriyaro, inda ya yi mata bayanin cewa, tana tattare da matsala a mahaifarta dan haka akwai bukatar yazo gidanta ya yi mata addu’a,  nan take ta amince ta ba shi kudi Naira 3050 da kuma tirare na Naira dubu xaya da ya bukata, “Bayan nan ya ziyarci matar a gidan ta inda ya ce ta tube kayanta ya shafa mata man zaitun a al’aurar ta da damatsanta yayin da ya ce, ta kalli littafin Bible da ya sanya a gaban ta, ya ci gaba da shafa mata man zaitun a damatsanta ta baya ko da ta juyo sai ta ga abin da yake sai ta ga ya fito da al’uransa  yana sanya man zaitun a jiki har ya zubar da mani inda ya tafi bandaki ya wanke, ganin haka sai ta gane cewa, ba faston kirki bane, ta ce da zai tafi ya fada mata yana son ya aure ta, dan haka yana bukatar ya dinga saduwa da ita.”

DSP Bala Elkana, ya kara da cewa bayan kwana daya faston ya koma gidan matar inda ya nemi ya yi lalata da ita sai ta kwarma ihu lamarin da ya sanya makwabta suka kawo mata dauki inda wasu da suka fusata suka yi wa faston duka har sai da jami’an ‘yan sanda suka kwace shi kafin daga bisani su tsare shi inda ake tuhumar sa da cin zarafin matar, aka kuma kulle shi a gidan yari na kirikiri.