Mutum biyu sun mutu wasu biyar kuma sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar tukunyar gas a yankin Orile-Iganmu da ke Karamar Hukumar Ifelodun, Jihar Lagos.
Wakilinmu ya ruwaito cewa daya daga cikin mamatan mai suna Ajibola Olaoye, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake aikinsa na walda a wata babbar na’ura.
Kakakin hukumar agaji ta jihar Legas, (LASEMA) Nosa Okunbor ya ce, “Lamarin ya faru ne a lokacin da mai waldan yake aiki kan wata babbar na’ura a garejin manyan motoci a gaban Kamfanin Atlas.
“Abun ya kashe shi nan take, wasu mutum shida sun samu munanan raunuka, an gaggauta kai su asibiti mafi kusa, inda dayansu ya cika”, inji shi.
Okunbor da shaidu sun ce fashewar tukunyar gas din ta faru ne sakamakon yoyon da tukunyar gas din da mamacin ke amfani da shi a lokacin da yake tsaka da aiki.
Ya ce jami’an kashe gobara da ‘yan sanda sun killace wuri domin kashe wutar da kuma hana ta bazuwa, yayin da aka riga aka hannanta gawar mamacin mai shekara 35 ga danginsa.
Sai dai bai yi karin haske a kan daya wanda ya rasu sakamakon raunin da ya samu daga iftila’in ba.
A ranar Talata da ta gabata ma wata fashewar tukunyar gas ta yi ajalin wata uwa da diyara da mai sana’ar hannu a rukunin gidaje na Ajao Estate a jihar ta Legas.