Wani farfesa a bangaren shari’a, Yemi Akinseye-George (SAN), ya fada wa Aminiya cewa ba zai yiwu Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Femi Otedola ba, kan ba da cin hanci.
Ya bayyana hakan ne bayan wata Babbar Kotu ta yanke wa Farouk Lawan — tsohon Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Binciken Badakalar Kudin tallafin mai — hukuncin daurin shekara bakwai kan karbar toshiyar bakin Dala 500,000 daga wurin Otedola.
Femi Otedola hamshakin dan kasuwa ne mai dillancin mai, wanda bidiyo ya nuno yana bai wa Faruk Lawan cin hancin na Dala 500,000, domin kwamitin da Faruk Lawan din yake jagoranta da ya cire sunan kamfanin Otedola na Zenon Oil daga jerin kamfanonin da ake bincike a badakalar.
A cewarsa, “Wanda ya ba da hancin ba shi da abin nan da a shari’a muke kira ‘niyyar aikata laifi’.
“Ya san ba shi da niyyar ba da hanci shi ya sa ya sanar da hukumomin tsaro domin su san da abin; Don haka, ba shi da niyyar aikata laifi kuma in babu niyyar to doka ba za ta hukunta shi ba,” inji Farfesan.
Ya ce kafin a ce an aikata laifin cin hanci da rashawa, lallai ne sai an samu abu biyu: nufi da kuma aiki na zahiri.
“Lamarin farko shi ne niyyar zuci na mai bayarwan a lokacin da ya bayar da hancin. A wannan batun babu niyyar aikata hancin.
“Hujjar da ake da ita a nan ita ce ta zahiri, wacce kuma hukumomin tsaro suna sane da ita.
“Wannan ne ya sa a wannan shari’ar ba ka da ikon cewa a hukunta wanda ya bayar da hancin saboda niyyarsa ba ta ya ba da rashawa ba ce, maimakon haka ma so yake ya bankado masu karbar hancin.”
Lauya Akinseye-George, wanda ke cikin wadanda suka rubuta daftarin Dokar Hukunta Manyan Laifuka (ACJA), ya ci gaba da cewa Faruk Lawan din yana da damar ya nemi beli bayan hukuncin da kotun ta yanke masa.
Amma ya ce sai kotun ta ga dama za ta ba da belin idan ya iya cika wasu sharudda, babba daga ciki shi ne rashin lafiya.
Sannan ya ce zai kuma iya daukaka kara har zuwa Kotun Koli ko kuma ya bukaci a sake nazarin shari’ar da aka yi masa.