✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesar da aka kora kan batanci ga Annabi za ta maka jami’arta a kotu

Ta ce sam korar za ta iya jawo mata bakin jini a nan gaba

Erika Lopez Prater, Farfesar nan da aka kora daga Jami’ar Hamline da ke Amurka saboda nuna zanen Annabi Muhammad (S.A.W) yayin koyarwa ta ce za ta maka makarantar a kotu.

Jami’ar dai, wacce mai zaman kanta ce a birnin St Paul na Jihar Minnesota a Amurka, ta yanke shawarar korar malamar ne bayan korafin da ta samu daga daya daga cikin dalibanta kan nuna hoton.

Erika Lopez dai ta nuna hoton ne a daya daga cikin azuzuwan da take koyar da Tarihi, lamarin da bai yi wa dalibai Musulmai na ajin dadi ba.

Ga Musulmai da dama dai, nuna hoto ko wani zane da ke nuna Annabi haramun ne kuma suna daukarsa a matsayin batanci ga addininsu.

Sai dai a kwafin karar wacce malamar ta ce nan ba da jimawa ba za ta shigar, ta jaddada cewa ba ta aikata ba daidai ba, saboda sai da ta yi gargadi kafin ta nuna hotunan, ta yadda ko da wani ba ya son ganin su zai iya fita.

Karar ta kuma yi zargin cewa korar ta jawo wa Erika matsala a rayuwar aikinta a matsayin malama, kuma hakan na iya jawo mata tsangwama da bakin jini a nan gaba.

Lauyoyin Farfesar, sun fada a cikin sanarwar cewa, “Daga cikin abubuwa da dama, hukumomin Jami’ar Hamline sun gwammace su shafa wa Erika Lopez kashin kaji, ta hanyar bayyana ta a matsayin wacce ya tsani Musulunci.

“Jawabai irin wadannan da aka riga aka wallafa su a kafafen yada labarai da dama na duniya, za su ci gaba da bibiyar Farfesa Erika har kashen rayuwarta, kuma za su iya kawo wa rayuwar aikinta cikas a ko ina,” in ji wani bangare na sanarwar.

Lamarin dai wanda ya faru a watan Oktoban bara, ya jawo zazzafar muhawara kan yadda ake nuna fifikon addini a makarantu, kodayake daga bisani makarantar ta yi fargar-jaji wajen daukar matakin korar malamar.