Duk da matsayinsa na shehin malamin jami’a, Farfesa Ahmed Abu Bilal na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, yana gudanar da sana’ar ta aikin walda a gefen titi.
Farfesa Ahmed Abu Bilal mai walda a gefen wani titi, malami ne a fannin lanarki da kayan laturoni, amma ya ce kudin da yake samu a wata daga sana’ar ya nininka albashinsa na farfesa.
A hirarsa Aminiya, farfesan, ya bayyana cewa Allah Ya ba shi basirar aikin walda, wadda yake alfahari da ita a matsayin abin biyan bukatunsa na yau da kullum kuma abin dogaro da kai a gareshi.
Ya ce duk da cewa a gefen hanya yake gudanar da sana’arsa, komai na tafiya cikin nasara ba tare da wata matsala ba.
Ya ce da farko ya yi karatu a fannin da ba na kimiyya ba, amma sai abokansa suka rika yi masa ba’a, duk da kyakkyawar sakamakon da ya samu, hasali ma suka ki taya shi murna.
- DSS za ta fara kerawa da sayar da jirage marasa matuka
- Lauyoyin Arewa za su maka gwamnati a kotu kan kisan Tudun Biri
Acewarsa, wannan dalili ne ya sanya shi ya koma bangaren kimiyya, inda ya faro daga matakin karatun sharar fagen karatun kimiyya.
Bayan shekara daya sai ya rubuta jarabawa kammala sakandare, bisa hukuncin Allah, sai ya zamo dalibi da ya fi kwazo a cikin duk daliban da suka rubuta jarabawar tare.
Wannan ne ya ba shi damar samun samun gurbin karatu a Jami’ar Ahmadu Bello a fannin na’urorin Lantarki da sauran na’urori.
Bayan ya kammala karatu da sakamakon mafi daraja, sai jami’ar ta dauke shi aikin koyarwa, inda ya ci gaba da karo karatu har ya zama farfesa a fannin.
Ya ci gaba da cewa, shi mutum ne mai matukar kaunar sana’ar hannu, wanda hakan ya ba shi damar koyar da dalibansa karatu a aikace.
Yadda na fara sana’ar walda
Ya ce, “Kasancewar muna harkokin koyarwa da kayayyaki na walda shi ne ya ba ni dama muke yi tare da dalibaina, wadanda suke da hazaka kwarai.
“Muna cikin wannan hali ne sai mutane daga wajen jami’a suka fara kawo aiki ana yi musu suna biya, amma daga baya sai hukumar jami’a ta hana, a maimakon ta hada hannu da ni mu ci gaba domin samar da kudaden shiga ga jami’ar, amma sai suka ki.”
Ya ce bayan da ya fito wajen jami’ar a kokarinsa na neman wurin da zai gudanar da sana’arsa, dole ta sanya shi farawa daga farko saboda rashin isassun kayan aiki da zai gudanar da sana’arsa yadda ya kamata, amma a dan kankanin lokaci al’amrra suka daidaita, aiki ya ci gaba da bunkasa.
Malamin Jami’ar ya ce kudin da yake samu a wata ya rubanya albashinsa na farfesa.
Ya ce wannan yana nuni da muhimmancin aikin hannu wanda ya kamata mutane su runguma.
Ya Kuma yi bayanin cewa yanzu haka yana kera kayayyaki na masu haka rijiyoyin burtsatse da injunan casar shinkafa.
Sannan yana aikin canza janaretocin bayar da wutar lantarki daga masu amfani da fetur zuwa na gas saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita.
A halin da ake ciki yanzu shi ne samun tallafi daga gwamnati domin bunkasa wajen sana’ar tare da horar da matasa masu sha’awar shiga cikinta da yawa.
Game da yadda kwararru ke yin kaura daga Najeriya zuwa wasu kasashe domin aiki, Farfesa Bilal ya ce ba shi da wata niyya ko tunanin barin Najeriya zuwa wata kasa.
Ya abin da zai kai shi wata kasa kawai shi ne don karo fasaha ba domin ya kara bunkasa sana’arsa ta yadda nan gaba za a rika dogaro da kayan da aka samar a Najeriya.
Kasata Najeriya it ace China da Jamus da Kuma Japan domin haka ya zabi ya tsaya domin ciyar da kasarsa gaba.
Malamin jami’ar ya ce “muna da kowadden irin mutane masu baiwa a Najeriya, wadanda idan gwamnati za ta tallafa musu, hakika Najeriya za ta sami bunkasa ta fannin kere-kere har a san ta a duniya.