✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin masara da shinkafa ya fadi a Saminaka

Akwai alamun al’ummar Najeriya musamman talakawa za su fara samun saukin rayuwa ta bangaren kayan abinci, saboda faduwar farashin kayayyakin abinci da aka fara samu,…

Akwai alamun al’ummar Najeriya musamman talakawa za su fara samun saukin rayuwa ta bangaren kayan abinci, saboda faduwar farashin kayayyakin abinci da aka fara samu, sakamakon fara shigowar kakar daminar bana.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a babbar kasuwar kayayyakin amfanin gona ta garin Saminaka da ke Jihar Kaduna wadda ta yi suna wajen tara kayayyakin amfanin gona musamman masara da kasuwar kayayyakin amfanin gona ta garin Jingir da ke karamar hukumar Bassa a Jihar Filato. Ya gano cewa farashin masara da shinkafa ya fadi kasa.
A baya ana sayar da buhun tsohuwar masara kan kudi Naira dubu 16, amma yanzu ana sayar da buhun tsohuwar  masara kan kudi Naira dubu 12 zuwa naira dubu 13.
Buhun sabuwar masarar da ta bushe  ana sayar da ita ne kan kudi Naira dubu takwas zuwa Naira dubu tara. A yayin da yanzu farashin buhun shinkafa sanfarera ana sayar da shi kan kudi Naira  dubu takwas, maimakon dubu  15 da ake sayarwa a baya.
A bangaren farashin mudun kayan abinci a wadannan kasuwanni  kuwa, yanzu ana sayar da mudun  masara tsohuwa kan farashi Naira 180 maimakon 220 da ake sayarwa ada. Mudun sabuwar masarar kuwa ana sayar da shi kan kudi Naira 150. Mudun tsohuwar shinkafa da ake sayarwa Naira 450 zuwa 470 ada yanzu ya dawo naira 380. A yayin da ake sayar da mudun sabuwar shinkafa Naira 330 zuwa 350.
A zantawarsa da wakilinmu kan wannan al’amari Sarkin Hatsi na Kasuwar Saminaka, Malam Manu Isah Idris ya bayyana cewa abin da ya kawo faduwar farashin kayayyakin amfanin gonar shi ne fitowar sabuwar masara.  Ya ce ana hasashe mai yiwuwa ne farashin kayayyakin amfanin gonar ya ci gaba da fuduwa saboda ci gaba da isowar amfanin gonar.