✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farashin man fetur zai iya kaiwa N340 a 2022 – NNPC

Ya ce daga 2022, gwamnati za ta cire tallafinta kwata-kwata a harkar fetur.

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari ya ce akwai yiwuwar farashin man fetur ya kai N340 a shekarar 2022.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya na watan Nuwamba a Abuja ranar Talata.

Ya ce babu makawa za a cire tallafin mai a cikin shekarar mai zuwa, kamar yadda doka ta tanada.

“Babu wata doka da za ta tanadi ci gaba da biyan tallafin mai, amma na tabbatar za ku yaba wa tsare-tsaren da gwamnati za ta bullo da su don jin dadin jama’a, da nufin ganin talakawa ba su sha wahala ba,” inji shi.

A kan batun hauhawar farashin iskar gas kuwa, Shugaban na NNPC ya alakanta hakan da tsanantar bukatar yawan makamashin a fadin duniya, inda ya ce yanzu haka kasashe da dama na fuskantar karancinsa.

Mele Kyari ya ce farashin na yin tashin gwauron zabo ne saboda babu tallafin gwamnati a cikinsa, sabanin a man fetur.

Sai dai ya ce NNPC na aiki tukuru wajen ganin ya samar da wadataccen makamashin na iskar gas.