A karon farko a cikin shekarar 2021, darajar danyen mai ya karu a kasuwar duniya inda farashin kowacce ganga ya haura $71.28.
Hakan na zuwa ne bayan taron Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur na Duniya (OPEC) da sauran mambobin kasashe a ranar Alhamis wanda ya ki amincewa da matsin lambar kara adadin gangunan da suke hakowa a kowacce rana.
- COVID-19: Abubuwa 7 da ya kamata Ku sani a kan rigakakin AstraZeneca
- Tashar tsandauri ta Kano za ta lakume Dala miliyan 27 kafin ta fara aiki
Farashin gangar dai ya karu ne da $1.28 (karin kaso biyu cikin 100) zuwa $63.98 a kan kowacce ganga a ranar Larabar da ta gabata.
Norbert Rücker, wani mai fashin baki a bankin kasar Switzerland na Julius Baer a ranar Laraba ya yi harsashen cewa akwai yuwuwar fasashin ya haura $70 kafin tsakiyar shekara.
“Muna harsashen karuwar farashin man na wucin gadi zuwa sama da $70 zuwa tsakiyar 2021,” inji shi.
Muna tafe da karin bayani…