Da alama kasashe masu arzikin man fetur sun shiga shekarar 2022 da kafar dama, bayan da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya karu zuwa Dalar Amurka 78.34 a kan kowacce ganga.
Tagomashin dai na zuwa ne gabanin taron Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) wanda za a yi ranar Talata.
- Abubuwa 18 da ya kamata ku sani game da marigayi Bashir Tofa
- ‘Yadda nake kai ’ya’yana daji ’yan bindiga suna lalata da su’
An samu kari farashin ne a karo na farko a sabuwar shekara, duk kuwa da yadda cutar COVID-19 ke ci gaba da shafar tattalin arziki.
Ana ganin karin farashin na da nasaba da takaita yawan man da ake hakowa a kasar Libya.
A wani labarin kuma, akwai yiwuwar OPEC ta tsaya a kan tsarinta na ganga 400,000 a kullum a cikin watan Fabrairu mai zuwa, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar.
A bara dai, farashin ya tashi da kusan kaso 50 cikin 100, a karon farko bayan da tattalin arzikin duniya ya fara farfadowa daga masassarar COVID-19, wacce ta tilasta rage yawan wanda kasashen ke hakowa.
Masana dai na harsashe cewa farashin zai iya faduwa a shekarar 2022, la’akari da yadda samfurin COVID-19 na Omicron ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya.