A kasuwar bayan fage ta ’yan canjin kuɗaɗen ƙetare a Najeriya, darajar Naira na ci gaba da ƙaruwa a yayin da farashin Dalar Amurka ke sauka.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan canjin ke sayen kowacce Dalar ɗaya a kan N1400 kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
- Gobara ta yi ta’adi a Kasuwar Idumota da ke Legas
- Majalisa Na Neman Ministan Lafiya Kan Badaƙalar Dala Miliyan 300
Wani binciken da shafin Nairametrics ya gudanar, ya bayyana cewa farashin Dalar na ci gaba da sulalowa ne sakamakon yadda mutanen da a baya suka ɓoye Dalar amma a yanzu suka fito da ita domin sayarwa sakamakon rashin daraja da dalar ke fuskanta.
Sai dai kuma kamar yadda binciken ya nuna, har yanzu ’yan kasuwar na sayar da Dalar a kan N1550 zuwa N1600.
A yayin zantawar jaridar da wani dan kasuwa mai suna Musa, ya bayyana cewa sun yi farin ciki da yadda farashin Dalar ke kara karyewa.
Musa ya bayyana cewa wannan zai ba su damar gudanar da kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali.
Sai dai har yanzu ana ci gaba da gudanar da canjin Dalar a kan N1560 a hukumance.