✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa na kokarin afka mana da yaki – Sojojin Nijar

Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar sun zargi kasar Faransa da jibge dakaru da makamai a makwabtanta da niyyar afka mata da yaki. Dangantaka dai…

Sojojin da ke mulkin Jamhuriyar Nijar sun zargi kasar Faransa da jibge dakaru da makamai a makwabtanta da niyyar afka mata da yaki.

Dangantaka dai ta yi tsami ne tsakanin Nijar da Faransa dai ta yi tsami ne tun bayan da sojoji suka kifar da Gwamnatin tsohon Shugaban Kasar, Mohammed Bazoumba watan Yulin da ya gabata.

A cikin wata sanarwa da aka yada a gidan talabijin din kasar ranar Asabar, Kakakin sojojin, Kanal Manjo Amadou Andulrahmane, ya ce, “Faransa ta ci gaba da jibge dakarunta a kasashen mambobin ECOWAS a shirye-shiryenta na kai mana hari, tare da hadin gwiwar kungiyar ta ECOWAS.”

Amadou ya kuma yi zargin cewa Faransar ta girke jiragen yaki da jirage masu saukar angulu da kuma motocin silke guda 40 a kasashen Ivory Coast da Jamhuriyar Benin.

“Akwai kuma jirgin daukar kaya na sojoji da ya dauko kayan yaki masu yawa da za a ajiye su a Senegal da Ivory Coast da Benin da dai sauransu,” in ji shi.

Tun bayan juyin mulkin dai Nijar ke zaman doya da manja da kungiyar ta ECOWAS, wacce ta yi barazana da karfin soji wajen afka wa kasar da karfin soji idan ba su dawo da Bazoum din kan mulki ba.

Sai dai kungiyar ta ce babbar fargabarta ita ce kada a maimaita abun da ya faru a kasashen Mali da Guinea da Burkina Faso, inda aka yi ta jan kafa kan lokacin mika mulki ga fararen hula.