✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fallasa a Katsina: Yadda Mahadi ya gurfana a gaban kotu

Mahadi ya hallara a kotu yana tafiya da kyar da sandar guragu

Dan kasuwa Mahadi Shehu da ya yi bidiyon fallasa da zargin zambar kudade a Gwamnatin Jihar Katsina ya gurfana a gaban kotu.

An ga Mahadi Shehu yana tafiya da kyar yana dogara sandar guragu a lokacin zaman Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta ta Katsina.

Gwamnatin Jihar Katsina ta yi karar dan kasuwar mazaunin Kaduna ne bis zarginsa da zambar intanet bayan jami’an tsaro sun tsare shi a Abuja.

Mahadi Shehu ana taimaka masa a lokacin da ya halarci zaman kotu.

Kwamishinan Shari’an Jihar, Ahmad El-Marzuq, ya yi karar Mahadi ne a watan Fabrairu, yana tuhumar sa da yada karairayi a kan Gwamnatin Jihar a shafukan sa da zumunta.

A cewarsa, takardun bayanan da dan kasuwar ya yi ta yadawa yake kuma dogaro da su wajen zargin almundahan, duk na jabu ne.

%d bloggers like this: