✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falalu dorayi ya yi nasiha kan muhimmancin Sallah

Fitaccen Daraktan Fina-Finan Hausa, Falalu dorayi ya yi nasiha mai kama jiki da hankali game da muhimmancin tsayar da Sallah. Daraktan wanda ya ba da…

Fitaccen Daraktan Fina-Finan Hausa, Falalu dorayi ya yi nasiha mai kama jiki da hankali game da muhimmancin tsayar da Sallah.

Daraktan wanda ya ba da umarni a manyan fina-finan da suka hada da ‘Alkibla’ da ‘Andamali’ da Namaliya ya ce Sallah daya ce daga cikin rukunnan Musulunci biyar. 

Falalu wanda ya taka muhimmiyar rawa a fim din ‘Umar Sanda’ ya kara da cewa Ubangiji (SWT) Ya wajabta guda 50 a kan bayinsa lokacin da Manzon Allah (SAW) ya yi Mi’iraji, amma cikin alfarma da tausayi irin ta Manzon Allah (SAW) sai aka rage wa bayi ita zuwa biyar.

Ya ce, Manzon Allah (SAW) Ya ce, “Ita ce farkon abin da za a yi wa bawa sakamako (hisabi) Ranar Al’kiyama. Idan ta yi kyau duk sauran aiki za su yi kyau, Idan ta yi muni to sauran ayyukan bawa ba za su amfane shi ba.”

Daraktan ya bayyana cewa Sallah tana karbuwa in an yi ta cikin natsuwa da ikhlasi, sannan ta dace da yadda Manzon Allah (SAW) ya karantar da ita.

Ya ce, “Ma’aiki (SAW) ya ce: ‘Ku yi Sallah kamar yadda kuka ga ina yin Sallah.” Falalu dorayi ya kara nanata cewa an wajabta yin Sallah a cikin jama’a, wato jam’i a masallaci.

Daraktan  ya ce duk wanda ya bar Sallah, to ya bar Musulunci.

Ya ce Manzon Allah (SAW) Ya ce: “Alkawarin da ke tsakaninmu da su shi ne, Sallah duk wanda ya bar ta to ya kafirta”. 

Falalu ya karafafa cewa wajibi ne kowane Musulmi ya san mece ce Sallah, ya kuma san hukunce-hukuncenta da abubuwan da suke bata ta da kuma abubuwan da suke inganta ta domin ta zamo karbabbiya a wajen Ubangiji Madaukaki.