Ga wasu daga cikin ayyukan falala da suka kebanci kwanaki goma na farko a watan Zul Hijjah.
Mun tattaro su ne daga hudubar Juma’a da Shaikh Abdul-Muhsin Al-Qasim ya gabatar a Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina a kasr Saudiyya a ranar Juma’a 3 ga Zhul Hijjah, Hijiriyya 1441.
Darajar kwanaki 10 na farkon watan ta fi ta kwanaki 10 na karshen watan Ramadan.
Dalilin haka kuwa shi ne, a cikin wadannan kwanakin ne ake gudanar muhimman ayyukan ibada: sallah da azumi da sadaka da kuma Hajji.
Hakan ba ya samuwa in banda a wadannan kwanakin.
Daga cikin ayyukan da aka kwadaitar da aikata su – akwai yin azumi a kwanaki tara na farkon watan.
Imam An Nawawi (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Ana matukar kwadaitarwa a kan haka”.
Bayar da sadaka abu ne mai kyau, kuma ana yaye bala’o’i sakamakon bayar da sadakar.
Lokacin da sadaka ta fi muhimmanci shi ne lokacin da ake tsananin bukatarta da kuma lokuta masu falala.
Tuba zuwa ga Allah tana da muhimmanci sosai a addini kuma samar da nasara da kuma farin ciki.
Allah Madaukaki Ya sanya tuba wajibi kan kowane zunubi a kan dukkanin mutane.
Daga cikin kwanakin 10 na Zhul Hijja, akwai ranar Arafat. Azumtar wannan ranar na sa a yafe wa bawa zunubansa na bara da na shekarar da ake ciki.
“Babu ranar da Allah Madaukakin Sarki Ke ‘yanta bayinSa daga wuta — kamar a wannan ranar ta Arafah”, kamar yadda Muslim ya ruwaito.
A ranar yanka, da kuma sauran kwanaki biyu na babbar Sallah, akwai wasu ayyukan ibada da suke da nasaba da arziki da jikin mutum:
Yanka dabba: yana daga cikin muhimman ayyukan da Allah Ya fi so.
Allah Ya ambace shi tare da sallah, inda Ya ce: “Ka yi sallah tare da yin yanka saboda Shi”. Sura ta 108 Aya ta 2.
Jaddada ikhlasi a hadayar da mutum zai yi.
Lallai ne mai yanka ya tabbatar da ya tsarkake niyyarsa domin Allah.
Kar ya zama mutum ya yi lauya ne domin riya ko cin nama ko son a san cewa shi mai hali ne ko kuma domin wata al’ada ko halayya.