✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faduwar darajar Naira ya sa farashin mota ya tashi

Alhaji Salisu Abdullahi na daya daga cikin ’yan Najeriya masu hada-hadar motoci daga kasashen waje zuwa kasar nan. A hirarsa da Aminiya ya koka kan…

Alhaji Salisu Abdullahi na daya daga cikin ’yan Najeriya masu hada-hadar motoci daga kasashen waje zuwa kasar nan. A hirarsa da Aminiya ya koka kan yadda faduwar darajar Naira ta jefa tattalin arzikin kasar nan cikin mawuyacin hali, inda hakan ya sa kasuwarsu ta tsaya cik. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu fara da gabatar da kanka?
Sunana Alhaji Salisu Abdullahi, na fara hada-hadar saye da sayar da motoci daga Kotono ko daga kasashen Turawa a karkashin Kamfanin Continental Motors da ke kan titin Sultan a Kaduna.
Ta yaya faduwar darajar Naira ta shafe ku masu sayar da motoci?
Lallai faduwar darajar Naira ta jefa mu cikin mawuyacin hali, inda harkar ta koma kusan babu uwar kudi ballantana riba. Motar da muke sayowa a da a kan Naira miliyan daya, yanzu ta koma Naira miliyan daya da dubu dari uku. To ka ga kasuwa ta yi kasa ke nan ga mai saye da kuma mai sayarwa.
Ko hakan ya sa ’yan kasuwa suka daina sayo motoci ke nan?
kwarai kuwa, don babu riba, ga kuma rashin tabbas. Dalili shi ne Naira kara faduwa take yi. To yaya za ka yi da biyan kudin fito da sauransu?
To ya kuke samun motocin da kuke baje-kolinsu?
Muna samu ne daga wurin wadanda suka sayo motoci da yawa suka tara kafin faduwar Naira. Su muke bi muna yin sari a wurinsu don mu nemi abin za mu sa a-bakin-salati.
Me ya sa kuka fi shigo da mota ta kasar Nijar?
Dalilin shi ne, ta Nijar an fi samun saukin kudin fito. Don ta iyakar Najeriya da Legas watau Seme akwai tsada sosai. Shi ya sa hukumar Kwastam ta sa kudin Seme ya fi na Katsina ko Sakkawato tsada, don motar ta biyo ta inda babu hada-hada sosai.
Mene ne ra’ayinka dangane da kafa kamfanonin hada motoci a kasar nan?
Rashin hangen nesan Gwamnati ne har ta yi tunanin cewa wani zai zo kasar nan ya rika hada mana motoci. Don ’yan Najeriaya ba za su iya sayen sabuwar mota ba, saboda lalacewar tattalin arzikinmu. Wanda yake da hali ne zai iya sayen irin wacce muke sayowa mu sayar, wato wacce ake kira ’yar kwatano ko Tokunbo, dalili shi ne tsadar sayen kayan aiki da rashin kishin hukumomin gwamnati da rashin wutar lantarki da haraji da sauransu. Kamfanonin hada motoci sun rufe tuntuni. Kamfanin Peugeot (Pijo) shi ma rarrafe yake yi, don ’yan kasa ba sa iya sayen sabuwar mota kirar Peugeot.
Wadanne kamfanonin hada motoci ne suka rufe?
Kamfanonin su ne na bolkswagen a Legas da Leyland a Ibadan da Fiat a Kano da na Steyr a Bauchi dai sauransu.
Ko motocin da suke zirga-zirga a kan titunan Najeriya suna da lafiya kuwa?
Daidai-kudinka-daidai-shagalinka. Manyan motoci da kanana irinsu DAF da Leyland da MAN-Diesel da Toyota da Honda da sauransu ba a nan ake hada su ba.
Amma gwamnati ta ce an kawo kamfanonin kera mota Najeriya?
kerawa ko hadawa? A ko ina za a iya hada mota. Kamfanonin da gwamnati ke kurarin cewa suna kera motoci duk soki-burutsu ne, bigi-bagiro ake yi wa jama’a. In da gaske ne a farfado da wadanda suka durkushe mana.