✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faduwar darajar Naira ta kawo cikas a kasuwancinmu – Alhaji Sulaiman

Sakataren kungiyar Dillalan Mota ta kasa, Alhaji Sulaiman Ibrahim Kato, ya bayyana takaicinsa yadda faduwar darajar Naira ta janyo musu cikas a harkokin kasuwancinsu na…

Sakataren kungiyar Dillalan Mota ta kasa, Alhaji Sulaiman Ibrahim Kato, ya bayyana takaicinsa yadda faduwar darajar Naira ta janyo musu cikas a harkokin kasuwancinsu na shigo da motoci kasar nan.
Kato ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke cikin garin Minna, babban birnin Jihar Neja, a farkon makon nan.
Ya bayyana cewa tashin gwauron zabbi da Dalar Amurka ta yi ya zame musu babban kalubalen da suke fuskanta a kasuwancinsu.
“Idan a da kana sayen mota a farashi mai sauki to yanzu dole ka saye ta a farashin mai tsada ta yadda idan ka kawo babu wanda zai saya. Ka ga wannan babbar matsala ce,” inji shi.
Ya ce kodayake kungiyarsu ta dauki matakan da suka dace don shawo kan lamarin ta yadda mambobinsu za su samu saukin tafiyar da al’amuransu cikin sauki.
Ya kara da cewa kungiyarsu ta kafa kwamiti na musamman da ya ziyarci kasar Benin don tattaunawa da mahukunta da masu ruwa da tsaki a harkar mota.
Ya bayyana cewa tuni suka cimma matsaya da mahukuntan kasar Benin kan matsalolin da suke fuskanta na yadda ake karbar haraji mai yawa a hannunsu.
Daga nan sai ya nemi hadin kan jami’an tsaron shigi da fici na kwastam da su tallafa musu don cimma burin da suka sanya gaba na shigo da motoci masu inganci cikin kasar nan.
Ya bayyana cewa kungiyar ta dauki matakan da suka dace don kawo karshen sace-sacen motoci da ake yi a kasar nan.
Ya yaba wa yunkurin da gwamnatin tarayya take yin a karfafa gwiwar kamfanonin kera motoci na gida.
To amma ya bayyana cewa wajibi ne gwamnati ta dauki matakan da suka dace muddin tana so kwalliya ta biya kudin sabulu.