A halin yanzu dai an samu shekara 14 da dawowar mulkin siyasa a kasar nan kuma jam’iyyar PDP ta yi shugabanni har guda bakwai. Ahmadu Mu’azu shi ne shugabanta na takwas. Idan mun kididdige, idan ka raba 14 zuwa gida bakwai, za ka samu biyu ke nan; wanda haka ke nuna cewa kowane shugaba ya yi mulkin shekara biyu ke nan.
Kodayake tsawon da shugaba ya kwashe a kan mulki ba wani abin damuwa ba ne amma abin damuwar shi ne, shugabanni shida daga cikin bakwai din duk korar su aka yi daga mukaman nasu a sakamakon fushin Shugaban kasa ko kuma wani dalili na daban. Kanar Ahmadu Ali ne kadai ya sauka daga shugabancin jam’iyyar bisa ka’ida, bayan cikar wa’adinsa.
Abin ya faro ne ta kan marigayi Solomon Lar, wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar na farko, wanda ya dare karaga a yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Jos. Sai kuma na karshe, Bamanga Tukur, wanda aka uzura mawa ya sauka, a sakamakon rikicin da shi kansa ya haifar a jam’iyyar. Duk da ya zarce shekaru tamanin a duniya, ya yi zaton yana da sauran karsashin da zai yi wa Shugaban kasa hidima, ya zama dan amshin Shatansa, duk kuwa da cewa al’ummar kasa ba su amince da haka ba.
Tun lokacin da na ga Bamanga ya fara takin saka da gwamnonin PDP na ce lallai ba zai yi karko ba a mulkinsa. Kodayake wannan yunkuri da ya yi, shi ne babban dalilin da ya sanya masu goyon bayan Jonathan suka sanya ransu a inuwa, saboda sun yi na’am da yadda tsoho Bamanga ya rika jan ido ga gwamnonin, yadda ya rika taka musu birki, domin kuwa a baya gwamnonin ne ke da ra’ayi wajen tafiyar da jam’iyyar da gwamnati.
A wajen nuna tasirinsa, sai da ya kai ga dakatar da wasu gwamnoni, ya kuma kori wasu daga jam’iyyar. Wani abu kuma shi ne, shi dai ba zabensa aka yi ba, an dai tabbatar da shugabancinsa ne a wurin taron jam’iyyar na kasa. Hasali ma, ya fadi ne a zaben fidda gwani da aka yi a jihohin Arewa Maso Gabas, amma da batun ya zo Abuja sai aka wanke shi, aka tarairaye shi.
Lokacin da ya samu kansa bisa kujerar mulkin PDP, sai ya fara zama zaki, ya dauki turbar tankwasa gwamnonin jam’iyyarsa domin su amince da takarar Jonathan a karo na biyu. Wannan shi ne babban kuskuren Bamanga!
Tun da farko dai marigayi Solomon Lar, a matsayinsa na shugaban jam’iyyar PDP, a matsayinsa kuma na dattijo, ya rike girmansa, ya ki yarda Obasanjo ya juya shi yadda yake so, don haka lokacin da suka kafa gwamnati, sai aka kore shi, aka maye gurbinsa da Barnabas Gemade. Daga nan kuma sai Audu Ogbe, ingantaccen dan siyasar da ya dade yana burge ni tun lokacin da nake karatu a jami’a. A lokacin nan yana daya daga cikin matasan ministoci masu jini a jika a Gwamnatin Shagari, a shekarun 1980. Dukkansu, Shugaban kasa Obasanjo ya yi waje da su bisa dalilin da shi kansa ya bar wa sani. Ahmadu Ali ya shigo da’irar mulkin, ya ga abin da ya gani, ya yi biyayya, kamar yadda ya saba yi ga ubangidansa Obasanjo a kowane lokaci.
An gudanar da zabe a 2007 kuma dan takararsu na fama da laulayi, haka shi ma mataimakinsa, ba lafiyar ta ishe shi ba. Haka dai aka dora shugabancin Najeriya ga shugaban da ba ya da koda, yayin da mataimakinsa ba ya da hanta. Ana kan haka sai Allah Ya amshi ran Shugaban kasar, mataimakinsa kuma ya maye kujerarsa.
A tarihin jam’iyyar, lokacin takaitaccen mulkin Shugaba ’Yar’aduwa ne kadai PDP ta kasance da shugaba guda daya na tsawon shekaru biyu ba tare da canzawa ba. ’Yar’aduwa na mutuwa sai Jonathan da mukarrabansa suka cire bincent Ogbulafor daga shugabancin jam’iyyar, kawai saboda ya yi ta maza ya bayyana cewa, shugabancin Najeriya na Arewa ne a wancan karon. Daga lokacin ne aka canja shi, aka dora dan siyasa kuma likita, Okwesilize Nwodo; wanda shi ma bai dade ba saboda yana da tunanin canja tsarin tafiyar da jam’iyyar ta yadda za a gudanar a ingantaccen zabe, wanda zai zama mai daraja al’ummar Najeriya. Nan aka maye gurbinsa da Bamanga Tukur, wanda shi kuma ya kirkiri matsalar da ta yi sanadiyyar kawar da shi daga mulki.
Wadannan dalilai na sama su suka sanya jam’iyyar ta zama wata bambarakwai, wacce ta kasance wani gida mai dauke da rikice-rikce, wanda babu zaman lafiya a cikinsa. Ga dukkan alamu dai jam’iyyar ta sukurkuce, yadda akwai matukar wuya a ce ta gyaru, ta koma daidai.
Fadi tashin shugabannin jam’iyyar PDP
A halin yanzu dai an samu shekara 14 da dawowar mulkin siyasa a kasar nan kuma jam’iyyar PDP ta yi shugabanni har guda bakwai. Ahmadu…