✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadawar mota cikin rafi ta yi sanadin rasuwar mutum 3 da raunata 11 a Ogun

Wani hadari da ya rutsa da motar fasinja ta kirar Bas da ke kan hanyar zuwa Legas daga garin Ijebu-Ode a jihar Ogun ta yi sanadiyyar…

Wani hadari da ya rutsa da motar fasinja ta kirar Bas da ke kan hanyar zuwa Legas daga garin Ijebu-Ode a jihar Ogun ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 3 yayin da 11 suka jikkata, hadarin ya faru ne bayan da motar ta kwacewa wani direba, inda ta fada kogin Ososa da ke babbar hanyar nan ta Ijebu-Ode zuwa Shagamu.

Kwamandan shiyya na Hukumar kiyaye hadurra FRCN da ke kula da jihar Ogun, Clement Oladele, ya miqa saqon ta’aziyar sa ga iyalan wadanda suka rasa ransu, ya ce namiji daya ne da mata biyu kana wadanda suka jikkata mata 6 ne maza 5. Ya ce, hadarin ya faru ne sakamakom matsalar da motar ta haifar wanda za a iya alaqantawa da rashin kula na abin hawa inda ya gargadin direbobin motocin fasinja da su kula da abin hawan su tare da yin takatsatsan da tuki da lura duba da yanayi na damuna da ake ciki a yanzu.

Tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata babban asibitin garin Ijebu-Ode domin kula da lafiyar su yayin da aka aje gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.