✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar shugaban kasa na shirin sayar da asibitinta

Fardar Shugaban Kasa ta aiyana kudurinta na sayarwa ’yan kasuwa babban asibitinta da ke harabar fadar. Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Sashen Yada Labarai na…

Fardar Shugaban Kasa ta aiyana kudurinta na sayarwa ’yan kasuwa babban asibitinta da ke harabar fadar.
Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Sashen Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasar, Mista Attah Esa, ya fitar, ta nuna cewa Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasar, Mista Jalal Arabi shi ne ya tabbatar da shirin sayar da asibitin.
An gina asibitin ne don ya rika kula da shugaban kasa da mataimakinsa da iyalansu da kuma ma’aikatan fadar shugaban kasar.
Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasar ya bayyana cewa kula da manyan na’urorin gwaje-gwaje kawai ya na lashe kimanin biliyan biyu a wata.
Haka na faruwa ne yayin da majinyata ke korafin ana tura su wasu asibitocin a waje don yin gwaje-gwaje.