Kotu ta tisa keyar wata matashiya zuwa gidan yari saboda kai wa wata ’yar sanda hari a yankin A’jah da ke Jihar Legas.
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta gurfanar da matar mai shekaru 26 ne bayan da kyamara kan titi ta kama ta tana cin zarafin wata ’yar sanda.
Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana hakan ta ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu a shafinsa na X.
Hundeyin ya ce “Mun gurfanar da wata ’yar shekara 26 a gaban kuliya bisa mummunan hari da ta kai wa wata ’yar sanda, bayan da kyamara ta dauko hoton cin zarafin a ranar 21 ga Fabrairu, 2024.
- Yadda jami’an tsaro suka kwato mutane 10 da aka sace a Katsina
- ‘Yar Najeriya mai shekaru 19 ta lashe Gasar Alkur’ani ta Duniya
“Washegari aka gurfanar da ita a gaban kotun majistare ta Etiosa, Ajah, kuma an tasa keyarta zuwa gidan yarin Kirikiri har zuwa ranar zama na gaba, 27 ga Maris, 2024.