✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EU za ta kakaba wa Iran sabbin takunkumai

A baya-bayan nan ma Iran ta rataye sama da masu bore hudu.

Kungiyar Tarayyar Turai EU na shirin kakaba wa Iran sabbin takunkumai kan abin da suka kira take hakkin bil’Adama da ake yi a kasar.

A wannan Litinin din ce ake sa ran ministocin kasashen ketare na EU a hukumance za su rattaba hannu a kan sabbin takunkumai da suka lafata wa wasu jami’an kasar Iran.

Jami’an diflomasiyyar na EU sun ce kusan mutum 40 da kamfanoni da kungiyoyi ne wannan sabbin takunkuman za su shafa bisa take hakkin al’umma da suka ce ana yi a kasar ta Iran.

Tun a watan Satumba bayan zanga-zangar da ta barke a kan mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami’an gyara hali na Hisba, Tehran ke amfani da karfi tana murkushe masu boren.

Rahotanni sun ce a baya-bayan nan ma ta rataye sama da masu boren hudu.

Ko baya ga wadannan takunkuman, ministocin na tafka muhawarar ayyana jami’an hisba Iran a matsayin ’yan ta’adda.