✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Shugaba Buhari ya gana da Ministan tsaro

Wata majiya ta ce sun tattauna ne a kan yadda zanga-zangar #EndSARS ke daukar sabon salo

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Gabriel Olonisakin.

Sun yi ganawar ta sirri ne ranar Talata a Fadar Shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Ba a fitar da wata sanarwa a hukumance game da tattaunawar ba.
Sai dai wata majiya a Fadar ta ce tattaunawar ta mayar da hankali ne a kan yadda zanga-zangar #EndSARS ke daukar sabon salo tana bigewa da tashin-tashina a sassan kasar da dama.
Kawo yanzu dai an ayyana dokar hana walwala a jihohin Edo da Legas da Filato da Osun da kuma Ondo, bayan da aka yi zargin cewa wasu bata-gari sun karkatar da akalar zanga-zangar zuwa fashe-fashe da kone-kone da ma kashe-kashe a wasu wurare.