✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Kwamitin bincike ya dage zamansa

Kwamitin ya dage zamansa da mako guda bayan wata wakiliyar matasa ta kaurece masa.

Kwamitin shari’ar binciken hatsaniyar zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Jihar Legas ya dage zamansa zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.

Matakin na zuwa ne bayan daya daga cikin wakilan masu zanga-zangar #EndSARS a zaman Oluwarinu Oduala ta kaurace wa wa zaman a safiyar Asabar.

Oluwarinu Oduala ta ki halartar zaman ne saboda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya rufe asusun bankin ta tare da na wasu jagororin zanga-zangar guda 18 bisa umarnin Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja.

Sakamakon haka, shugaban kwamitin, Mai Shari’a Doris Okuwobi (mai ritaya) ta sanar da dage ci gaban zaman zuwa ranar Asabar 14 ga Nuwamba, 2020.