A ranar juma’a gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gabatar masa da rahoton irin barnar da bata-gari suka yi a jiharsa
Fadar gwamnatin tarayya ta bayyana a shafinta na Twitter cewa shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan wanda kuma ya gabatar masa da rahoton yadda rikicin #EndSARS ya shafi jihar.
- Sai da na kusa zubar da hawaye ganin yadda aka yi wa Legas — El-Rufa’i
- #EndSARS: Ministoci da gwamnonin Kudu sun ziyarci Legas
- Zanga-zangar EndSARS ta jawo asarar biliyan N400 a Legas
- ‘Labarun karya ne suka haifar da rikici a Legas’
A ranar Larabar da ta gabata ne ministoci daga yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya suka bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki lamarin da ya faru a Lekki.
Sai dai shugaba Buhari ya bawa dukkan ministoci wa’adin mako guda kan kowannensu ya koma jiharsa don ya jawo hankalin mutanensa kan illar tashin hankali.
Shugaban ya kuma umarci ministocin su gabatar da rahoton shirin da suka yi na kawo zaman lafiya a fadin kasa.
Zanga-zangar da aka faro ta domin neman kawo karshen zaluncin bangaren ‘yan sanda na SARS dai daga baya ta rikide inda bata-gari suka shiga satar kayan mutane tare da lalata dukiyoyin al’umma da na gwamnati a sassa daban-daban na Najeriya.
Sai dai gwamnatin tarayya na ganin cewa labarun karya da ake yadawa a kafafen sada zumunta sun yi tasiri sosai wajen tada fitina a lokacin zanga-zangar.
Wanda hakan ne yasa gwamnati ta fara tunanin kafa dokar sanya ido akan kafafen sada zumuntar.