✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EndSARS: Dalilin da ya hana Buhari magana a kan harbin Lekki

’Yan Najeriya sun soki Shugaban Kasar dangane da rashin magana ta nuna tausayi ko jajantawa.

Babu abin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ambata game da harbin masu zanga-zangar #ENDSARS da jami’an tsaro suka yi a Lekki a daren ranar Talata yayin da ya gabatar da jawabansa ga ‘yan kasa a ranar Alhamis.

Fadar Shugaban Kasa ta ce Shugaba Buhari bai ce uffan ba sakamakon dalilai na rashin tabbas don gudun fadin abin da ba haka ba.

’Yan Najeriya da dama sun soki Shugaban Kasar dangane da rashin magana ta nuna tausayi ko jajantawa wadanda mummunan tsautsayin ya auku a kansu.

Sai dai a wani shiri na gidan talbijin din Channels da mai magana da yawun shugaban kasar Mista Femi Adesina ya bayyana, ya ce Shugaban Kasar ba ya da damar fadin komai a kan harbe-harben sakamakon bincike da masu ruwa da tsaki ke gudanarwa.

“Rundunar Dakarun Tsaro ta Kasa ta fidda sanarwar cewa tana gudanar da bincike a kan lamari, kazalika, Gwamnatin Legas ta kafa kwamitin bin diddigin gano hakikanin abin da ya faru.”

“Saboda haka Shugaban Kasa ba ya da ikon fadin komai a kan lamari don duk abin da ya fada zai iya zama akasin gaskiyar yadda lamarin ya kasance bayan bincike bai kammala ba.”

“Sai bayan an kammala bincike ne Shugaban Kasar zai samu damar yin ambato game da lamarin,” inji Mista Adesina.