Gwamnatin Jihar Legas ta umarci a yi bincike kan harbe-harben da aka yi a kan masu zanga-zangar EndSARS a unguwar Lekki da ke Jihar.
Jami’an tsaro sun bude wuta bayan masu zanga-zangar EndSARS sun bijire wa dokar hana fita a jihar, lamarin da ya sa masu zanga-zangar guje-guje wasunsu kuma suka dage cewa ba za su watse ba.
“Yanzun nan na kammala duba wadanda harbin Lekki ya shafa shi ya sa na dau lokaci ban yi jawabi ba saboda dole in ba wa rayuwar mutanen da abin ya shafa muhimmanci.
“A matsayina na Gwamna alhakina a kaina kuma zan yi aiki da Gwamnatin Tarayya domin gano tushen matsalar tare da tabbatar da daidaituwar tsaro domin kare rayukan jama’armu”, inji Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Bayan aukuwar lamarin, gwamnan ta bakin Kwamishinan Watsa Labarai, Gbenga Omotoso, ya bukaci jami’an tsaro da kada su tsare masu karya dokar.
Ya kuma bukaci jama’ar jihar su bi dokar domin a samu kwanciyar hankali sannan su guji bayar da damar da miyagu za su yi amfani da ita wajen tayar da zaune tsaye.
“Gwamna zai yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da kariyar jama’ar jihar Legas a kowane lokaci”, inji sanarwar.
Ya ce mutum 27 ne suka samu raunuka sakamakon hatsaniyar amma an sallami uku daga cikinsu.
Gwamna Sanwo-Olu ya ce 10 daga cikinsu na Babban Asibitin Jihar, wasu 11 a Asibitin Reddington sai kuma wasu mutum hudu a Asibitin Vedic.
“Zan ci gaba da lura da yanayin”, inji shi.