✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Emenike ya yi ritaya daga Super Eagles

Dambarwar da ke tsakanin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da wasu daga cikin ’yan kwallonsa ta sake faruwa bayan dan kwallon gabansa Emmanuel…

Dambarwar da ke tsakanin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da wasu daga cikin ’yan kwallonsa ta sake faruwa bayan dan kwallon gabansa Emmanuel Emenike ya bayar da sanarwar yin ritaya daga kungiyar.

Kamar yadda kafar sadarwa ta Premium Times ta kalato a ranar Litinin da ta wuce, dan kwallon ya bayar da sanarwar yin ritaya daga Super Eagles a wani sako da ya aika ta kafar sadarwarsa ta Instagram inda ya ce ya yi ban kwana da Super Eagles.
dan kwallon da yanzu haka yake buga wa kulob din Al-Ain na Dubai bayan kulob dinsa na asali Fenerbache da ke Turkiyya ya bayar da shi a matsayin aro ga kulob din na Dubai ya fitar da wannan sanarwa ce a daren Litinin da ta gabata. Ya ce: “daga yau na daina buga wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wasa. Na share kimanin shekara biyar ina buga mata kwallo, don haka ina mai matukar farin cikin sanar da jama’a cewa daga yau na daina buga wa kungiyar kwallo. Na dauki wannan mataki ne don na kawo hadin kai da kuma zaman lafiya a kungiyar”.
Ya kara da cewa, “ina alfahari da na shafe akalla shekara biyar ina yi wa kungiyar kwallo ba tare da matsala ba, kuma ban taba yin nadama ba, don haka ina mika godiyata ga miliyoyin ’yan Najeriya musamman magoya bayana a lokacin da suka kasance tare da ni da dadi ba dadi”.
“Na yi murna da na samu lambar zinare a gasar cin kofin Afirka da ya gudana a 2013 kuma wannan ya nuna ba karamin nasara na samu a kungiyar ta Super Eagles ba”.
Ya ce “a iya saninsa, kungiyar Super Eagles ta kowa ce, ba ta wani mutum guda ba, don haka ban ga dalilin da zai sa a kyale wani ya rika juya mu yadda yake so ba tare da an taka masa birki ba”.
Sai dai wadannan kalamai da dan kwallon ya yi ana hasashen ya yi su ne sabiili da sabanin da ya samu a tsakaninsa da koci Sunday Oliseh al’amarin da ya sa ya dauki wannan mataki na daina yi wa kungiyar wasa.
Emenike dai yana daga cikin ’yan kwallon da suka samu nasarar lashe wa Najeriya kofi a gasar cin kofin Afirka da ta gudana a shekarar 2013.
Masana harkar kwallo na ganin Emenike ya yi murabus daga Super Eagles ne ganin yadda ya shafe kimanin shekara 2 ba tare da ya jefa kwallo daya a raga ba a matsayinsa na dan kwallon gaba (Striker). Ana ganin dan kwallon ya dade da tunanin yin ritaya daga kungiyar don haka ne ya yi amfani da wannan dama ya ajiye kwallon mangwaro don ya huta da kuda. Kawo yanzu dan kwallon ko Sunday Oliseh ba su fito sun bayyana sabanin da ke tsakaninsu ba.
Idan zaa tuna a watan da ya wuce ma golan Super Eagles bincent Enyeama ya yi murabus daga kungiyar Super Eagles bayan ya samu sabani da Koci Sunday Oliseh.