✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Zakzaky na nan bai rasu ba – IMN

Bai kamata Gwamnati ta yi kuskuren da Shugaban mu zai mutu a hannunta ba.

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da Shi’a, ta karyata rade-radin mutuwar shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Abdullahi Usman, wanda mamba ne a Kungiyar ya tabbatar wa Aminiya ta tarho cewar Malamin yana nan a raye.
“Ba san inda mutane suka samo jita-jitar ba don ina mai tabbatar muku cewar Shugaban mu na nan a raye.
“Bai kamata Gwamnati ta yi kuskuren da Shugaban mu zai mutu a hannunta ba” inji Abdullahi
Jita-jitar rasuwar Zakzaky ta bazu a cikin garin Kaduna wanda hakan ya sa mutanen takaita zirga-zirgarsu a cikin garin saboda gudun tashin hankalin da Kanu iya barkewa.